Da duminsa: Wata sabuwar cuta 'Marbug' mai kama da Ebola ta bulla a kasar Guinea, kusa da Najeriya

Da duminsa: Wata sabuwar cuta 'Marbug' mai kama da Ebola ta bulla a kasar Guinea, kusa da Najeriya

  • Wata biyu bayan gujewar Ebola a Guinea, sabuwar cuta ta sake bulla
  • Akalla mutum daya ya mutu kawo yanzu sakamakon cutar
  • Jami'an kiwon lafiya na neman mutane da suka hadu da marigayin don killacesu saboda dakile yaduwar cutar

Guinea - Wani mara lafiya ya kamu da wata cutar Marburg a kasar Guinea kuma ya mutu, a cewar jawabin da kungiyar lafiyar duniya ta saki ranar Litinin, 9 g Agusta, 2021.

CNN ta ruwaito cewa Wannan shine karo na farko da wata cuta mai kama da Ebola zata bulla a yankin yammacin Afrika.

An dauki samfurin Wannan cuta mai sanya mutum zazzabi daga jikin wani mara lafiya Gueckedou.

Jawabin ya kara da cewa bullar cutar nan na zuwa ne watanni biyu bayan kasar Guinea ta sanar da bacewar Ebola.

Jawabin yace:

"Gueckedou, inda aka tabbatar da cutar Marburg, ne yankin da aka samu cutar Ebola a 2021 da kuma shekarar 2014 zuwa 2016."

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

"Samfuran da aka dauka daga wannan marigayin na dauke da cutar Marburg bayan da akayi gwaji a Gueckedou."
"Hakazalika gwajin da akayi a Institut Pasteur ya tabbatar da hakan."

Jami'an kiwon lafiya a ranar Litinin na neman mutane da suka hadu da marigayin don killacesu saboda dakile yaduwar cutar.

Wata sabuwar cuta 'Marbug' mai kama da Ebola ta bulla a kasar Guinea, kusa da Najeriya
Da duminsa: Wata sabuwar cuta 'Marbug' mai kama da Ebola ta bulla a kasar Guinea, kusa da Najeriya Hoto: cnn.com
Asali: UGC

WHO ta tura masana 10 kasar Guinea domin binciken lamarin.

A cewar WHO, cutar ta samo asali ne daga cikin jemagu kuma tana iya bazuwa tsakanin mutum zuwa mutum ta zufar jiki ko idan yawun mutum ya fada kan abubuwa.

Kawo yanzu, babu rigakafin wannan cuta kuma babu maganinta, illa yan magunguna da ake baiwa masu fama da ita don rage radadi.

An fara gano cutar Marburg ne a 1967, inda mutane 31 sukayi rashin lafiya a Jamus da Yugoslavia inda aka gano cewa akwai cutar jikin birai a Uganda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel