Yanzu-yanzu: NCDC ta gargaɗi ƴan Nigeria kan yiwuwar sake ɓullar Ebola

Yanzu-yanzu: NCDC ta gargaɗi ƴan Nigeria kan yiwuwar sake ɓullar Ebola

- Hukumar NCDC ta gargadi yan Nigeria game da yiwuwar sake bullar cutar Ebola

- Hakan na zuwa ne sakamakon bullar cutar a kasar Guinea da ke kusanci da Nigeria

- Hukumar ta bawa al'umma tabaccin cewa tana cikin shiri kuma ta tanadi kayan aiki

Cibiyar Kare Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC, ta ce akwai yiwuwar annobar Ebola za ta iya sake bulla a Nigeria kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta tabbatar da babu Ebola a Nigeria a ranar 20 ga watan Oktoban 2014 bayan wani dan kasar Liberia, Patrick Sawyer ya shigo da cutar cikin kasar.

Yanzu-yanzu: Annobar Ebola na iya sake ɓarkewa a Nigeria, in ji NCDC
Yanzu-yanzu: Annobar Ebola na iya sake ɓarkewa a Nigeria, in ji NCDC
Asali: Twitter

Cutar ta yi sanadin rasuwar yan Nigeria da dama cikinsu har da Dr Stella Adadevoh wacce ta kula da Sawyer sannan ta hana shi barin asibitin Legas inda aka kwantar da shi.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga: Kungiyoyin Yarbawa da Ibo da Tsakiya sun yi wa Gumi kaca-kaca

A cikin sabon sanarwar da ta wallafa a shafinta, Hukumar NCDC ta ce akwai yiwuwar cutar ta sake bula a Nigeria duba da kusancinta da kasar Guinea inda a halin yanzu cutar ta bula.

NCDC ta ce tana da wata tawaga ta musamman mai aiki kan cututuka masu yaduwa da janyo zubar da jini (EVHDWG) da ke aiki kan ko-ta-kwana na bullar irin wannan annobar.

Hukumar ta bada tabbacin cewa ta dauki matakan sawwake illar da annobar ta Ebola za ta iya yi ko da an samu bullar ta a Nigeria.

KU KARANTA: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa

"Sashi na aikin gaggawa a NCDC na nan cikin shiri.

"Muna da tawagar masu kai taimakon farko a gefe da za a iya tura su suyi aiki a kowanne lokaci idan an samu bullar cutar a Nigeri.

"Mun kuma tanadi kayan gwaji a dakin gwaje-gwaje na NCDC. Hukumar za ta cigaba da aiki domin ganin Nigeria na cikin shiri," a cewar wani sashi na sanarwar.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164