Yawan cin 'ya'yan itace na haddasa babban cuta - Kwareren Likita
- Wani kwararen Likita, Farfesa Oladapo Ashiru ya gargadi al'umma kan ciye-ciyen 'ya'yan itace masu zaki da yawa a lokaci guda
- Farfesa Ashiru ya ce 'ya'yan itacen na dauke da suga wanda galibi ya kan yiwa jikin dan adam yawa kuma madaci ka kasa sarrafa shi
- Farfesa ya ce wannan dabi'a na markade 'ya'yan itatuwa masu zaqi da yawa waje guda a sha yana daya daga cikin abinda ke janyo ciwon suga
Wani kwararen likita, Farfesa Oladapo Ashiru ya gargadi 'yan Najeriya game da cin 'ya'yan itace fiye da kima inda ya bayyana cewa hakan na iya janyo ciwon suga (Diabetes) da masu matsalolin da jinkin dan adam.
Ashiriu wanda shine shugaban wani asbiti da ke jihar Legas, Mart-Life Detox Clinic ya kuma koka kan yadda 'yan Najeriya ke cin abinci marasa gina jiki.
Ya yi wannan jawabin ne a wata lakta da ya yi da wata kungiyar sai ka, The City Club da shirya a ranar Alhamis da ta gabata a Legas.
DUBA WANNAN: Dan takarar Sanata a APC ya maka jam'iyya a kotu bisa canja sunansa
A cewarsa, cin 'ya'yan itace da yawa bashi da kyau ga jikin dan adam kuna ya na daga cikin dalilin da yasa mutane da yawa su kan kamu da cutar suga.
Ya ce a yanzu mutane su kan hada 'ya'yan itace daban-daban kamar kankana, abarbar, lemu masu yawa sannan su markade shi waje guda su rika sha wanda a turence a ke kira "Smoothies".
Adadin suga da ke cikin 'ya'yan itacen su kan yiwa madacin jikin dan adam yawa dama madacin shi ke fitar da sinadarin insulin da ke sarrafa suga a jikin dan adam domin kada tayi yawa.
Likitan ya ce Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce adadin suga da mutum ke bukata a kullum bai wuce gram 200 wanda hakan kuma bashi da yawa.
Kwararen likitan kuma ya shawarci mutane su dena sauri idan suna cin abinci ma'ana su rika tauna abinci kafin su hadiye. Ya kuma shawarci mutane su rika amfani da abincin mu na gargajiya kamar wake, garri, aya, kwakwa da sauransu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng