An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO

An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO

An gano wani dauke da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo, lamarin da ya tayar hankulan jama'a a yayin da ake fama da annobar coronavirus.

Cibiyar lafiya ta duniya ta ce an tabbatar da samun mai cutar a wani birni mai suna Beni da ke gabashin jamhuriyar Congo.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mai dauke da cutar ya mutu ne a safiyar Alhamis a asibiti bayan ya nuna alamun cutar na kwanaki masu yawa.

Tabbatar da samuwar cutar ya zama koma baya ga jamhuriyar Congo a yayin da take kokarin yakar cutar coronavirus.

An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO

An samu bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo - WHO
Source: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan ya killace kansa

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, an sanar da hakan ne a yau Juma'a bayan mutuwar mai cutar a ranar Alhamis.

Baya ga barkewar Ebola, jamhuriyar Congo na fama da annobar coronavirus, kyanda da kuma cutar amai da gudawa wacce ta kashe dubban yara.

Mutane 215 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar. Mutane 20 suka rasa rayukansu yayin da 13 suka warke daga cutar.

Cibiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana Ebola a matsayin annoba tun bayan da cutar ta barke a 2019. Ta taba biranen Goma da wasu kasashe masu makwabtaka.

Har zuwa Juma'a, ba a samu wani wanda ya kamu da cutar ba tun daga ranar 17 ga watan Fabrairu.

"Binciken farko ya bayyana cewa mamacin mai shekaru 26 dan asalin yankin Beni ne," takardar kwamitin martanin gaggawa ta sanar.

"Kungiyarmu tare da hadin guiwar cibiyar kiwon lafiya ta duniya ta fara zurfafa bincike don aiwatar da matakan kiwon lafiya," ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel