Isra'ila Ta Yi Yunkurin Kashe Shugaban Iran a Dakin Taro, An Ji abin da Ya Faru
- Iran ta bayyana cewa za ta iya warware matsalolin da ke tsakaninta da Amurka ta hanyar tattaunawa duk da cewa akwai matsalar amana
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya roƙi shugaban Amurka, Donald Trump da kada ya bari Isra'ila ta zuga shi ya shiga yaƙi da kasarta
- Pezeshkian ya zargi Isra'ila da rushe tattaunawa ta hanyar kai hare-hare Tehran, har ma da yunkurin kashe shi a a lokacin da yake cikin taro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Iran - Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa yana da yakinin cewa Iran na iya warware sabanin da ke tsakaninta da Amurka ta hanyar tattaunawa.
Sai dai, Masoud Pezeshkian ya ce rashin yarda ne zai zama kalubale ga tattaunawar su da Amurka, duba da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa ƙasarsa.

Source: Twitter
Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne cikin wata hira da yayi da Tucker Carlson, ɗan jarida mai ra’ayin mazan jiya daga Amurka, a ranar Asabar, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Iran ta nemi tattaunawar sulhu da Amurka
Masoud Pezeshkian ya ce:
"Ina da yakinin cewa za mu iya warware bambance-bambance da rikice-rikicen da ke tsakaninmu da Amurka ta hanyar tattaunawa, hanya ce mafi sauƙi."
Shugaban Iran ya roƙi shugaban Amurka, Donald Trump, da kada ya bari Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, wanda zai kai ziyara fadar White House, ya zuga shi yin yaƙi da Iran.
"Shugaban Amurka, Trump, yana da ƙwarewar da za ta iya jagorantar yankin zuwa zaman lafiya, da kuma nunawa Isra’ila matsayinta. Amma kuma yana iya jawo komai ya lalace. Saboda haka, zabin yana hannun shugaban Amurka yanzu."
- Masoud Pezeshkian.
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce ba ta da tabbacin ko Trump ya ji kalaman shugaba Pezeshkian, amma ta amince cewa shi ne mutum mafi dacewa wajen kawo zaman lafiya a yankin.
Isra'ila ta yi yunkurin kashe shugaban Iran
Pezeshkian ya dora laifin rusa tattaunawar zaman lafiya a kan Isra’ila yana mai cewa Isra’ila ce ta fara kai hari ga Iran a ranar 13 ga Yuni, lamarin da ya haddasa yaƙin kwanaki 12 tsakanin ƙasashen biyu.

Source: Twitter
"Ta yaya za mu sake yarda da Amurka? Ta yaya za mu tabbata cewa yayin da tattaunawa ke gudana, ba za a ba Isra’ila damar sake kai mana hari ba?" inji Pezeshkian.
Har ila yau, shugaban ya zargi Isra’ila da yunkurin kashe shi, kamar yadda kafar watsa labarai ta Aljazeera ta ruwaito.
"Hakika sun yi ƙoƙarin hallaka ni. Sun yi shiri sosai, amma ba su samu nasara ba.
"Ba Amurka ce ke bayan yunkurin kasheni ba — Isra’ila ce. Ina cikin wani dakin taro… suka yi ƙoƙarin jefa bama-bamai a wurin da muke yin taron."
Isra’ila ba ta yi martani kai tsaye game da wannan zargi na cewa tayi yunkurin kashe shugaban Iran din.

Kara karanta wannan
'Ba haka ba ne,' Iran Ta yi martani bayan Trump ya ce zai zauna da ita kan nukiliya
'Trump ya rura rikicin Iran-Isra'ila" - China
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin China ta zargi shugaban Amurka, Donald Trump, da rura wutar rikicin Iran da Isra’ila, bayan da ya yi gargadi ga mazauna birnin Tehran.
Isra’ila ta kaddamar da hare-hare kan Iran a wani yunkuri na hana ta mallakar makaman nukiliya, lamarin da ya jawo barkewar yaki na kwanaki 12.
A martanin ta, China ta bayyana cewa amfani da zafafa harshe, barazana, ƙara matsin lamba da hura wutar rikici da Amurka ke yi ba zai haifar da da mai ido ba, illa dai ƙara tsananta rikicin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

