Shugaban Amurka Ya Tsallake Rijiya da Baya a Majalisa bayan Harin da Ya Kai Ƙasar Iran

Shugaban Amurka Ya Tsallake Rijiya da Baya a Majalisa bayan Harin da Ya Kai Ƙasar Iran

  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya tsallake yunƙurin tsige shi a Majalisar Wakilai kan hare-haren da ya kai ƙasar Iran
  • Ƴan Majalisar sun yi fatali da kudirin da aka gabatar na neman sauke Trump daga mulki kan laifin ɗaukar matakin soji ba tare da izini ba
  • A zangon mulkinsa na farko, Trump ya fuskanci tsigewa sau biyu a Majalisar Wakilai amma daga bisani Majalisar Dattawa ta wanke shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

USA - Majalisar Wakilai ta Amurka ta kada ƙuri’ar kin amincewa da kudirin tsige Shugaban Ƙasa, Donald Trump, kan hare-haren da ya kai Iran ba tare da izini ba.

Wannan mataki ya zo ne ba zato ba tsammani daga ɗan Majalisa ɗaya tilo, Al Green daga jihar Texas, wanda ya gabatar da ƙudirin tsige Trump bisa laifin karya dokar tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Murna ta ɓarke a Majalisar Tarayya da mambobi 2 suka ƙara kassara PDP, LP a Najeriya

Shugaban Amurka, Donald Trump ya tsallake kudirin tsigewa a Majalisa.
Majalisar Amurka ta yi watsi da kudirin tsige Shugaba Trump kan harin Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar AP News ta tattaro cewa tun farko kudirin tsige Trump ya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar Democrat.

Mafi yawan ‘yan Democrat sun haɗa kai da ‘yan jam'iyyar Republican wajen fatali da ƙudirin, yayin da wasu kuma suka amince a tuɓe shugaban ƙasar.

Sai dai a zaman ƴan Majalisar Wakilan Amurka na jiya Talata, sun yanke shawarar karshe kan kudirin, inda ƴan Majalisa 344 suka kaɗa kuri'ar watsi da kudirin, 79 suka goyi baya.

Dalilin gabatar da kudirin tsige Donald Trump

Da yake jawabi, ɗan majalisar da ya gabatar da kudirin tsige Trump, Green ya bayyana cewa:

"Na yi haka ne domin bai kamata mutum ɗaya ya yanke hukuncin shiga yaƙi a madadin mutane fiye da miliyan 300 ba tare da tuntubar Majalisar Amurka ba.

Wannan ba shi ne karo na farko da aka yi ƙoƙarin tsige Shugaba Trump ba tun bayan sake darewarsa kan mulki a wa’adi na biyu a watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kisan 'yan daurin aure a Plateau ya je kunnen Tinubu, ya ba da umarni

Sai dai hakan ya nuna yadda wasu daga cikin ‘yan Democrat ba su jin daɗin salon mulkinsa musamman bayan samamen gaggawa da ya kai kan wuraren nukiliyar Iran.

Trump ya soki wata ƴar jam’iyyar Democrat, Alexandria Ocasio-Cortez daga jihar New York, da kalmomi masu zafi bayan da ta ce matakin soji da ya ɗauka abu ne da za a iya tsige shi akai.

Majalisar Wakilan Amurka ta ɗauki matsaya

Shugabannin jam’iyyar Democrat a Majalisa ba su fito kai tsaye suka soki Al Green ba kan batun tsige Trump ba, amma sun nuna cewa ba wannan ne babban abin da suka sa gaba ba.

A halin yanzu dai, Majalisar ta yi watsi da wannan kudiri bayan kaɗa kuri'ar ƙin amincewa a zaman ranar Talata, kamar yadda Al-Jazeera ta tattaro.

Donald Trump ya tsira daga shirin tsige shi.
Msjalisar Wakilai ta janye yunkurin tsige Shugaba Trumo kan shiga yaƙi da Iran Hoto: Donald J. Trump
Source: Twitter

An tsige Trump sau biyu a wa’adin mulkinsa na farko da jam’iyyar Democrat ke da rinjaye a Majalisar Wakilan Amurka.

Sai dai a duka lokutan biyu, Majalisar Dattawa ta wanke Trump, abin da ya ba shi damar ci gaba da mulki a wannan shekara.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Iran ta ƙara yunƙurowa tun da asubah, ta yi ɓarin wuta kan Isra'ila

Trump ya fara maganar canza gwamnatin Iran

A wani labarin, kun ji cewa Donald Trump ya ce yana ganin ya kamata 'yan kasar Iran su sauya gwamnatinsu idan ta ki amincewa da tattaunawa kan shirin nukiliyarta.

Wasu majiyoyi sun ce Trump yana bukatar Iran ta yarda da mafita ta lumana ba tare da zubar da jini ba domin kawo ƙarshen wannan rikici.

Shugaban na Amurka ya ce matuƙar gwamnatin Iran ta ƙi yarda ta janye shirinta na samar da makaman nukiliya, to yana ganin ya kamata ƴan kasar su nemi canji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262