Air India: Kuskuren da Ake Zargin Matukin Jirgi Ya Tafka da Ya Jawo Mutuwar Mutum 241
- Ana zargin wani kuskure mai muni da ya faru yayin tashin jirgin Air India ne ya haddasa mummunan hadarin da ya yi ajalin mutum 241
- Wani masanin sufurin jiragen sama, Captain Steve, ya yi imani da cewa kuskuren matuki na kin dage tayoyin saukar jirgin ne ya jawo hadarin
- Sai dai, wannan ra'ayi ne na Captain Steve kawai, domin har yanzu hukumomi na ci gaba da gudanar da bincike don gano dalilin hadarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
India - Jirgin saman Air India ya yi hadari bayan tashinsa a ranar 12 ga Yuni, 2025, inda mutane 241 daga cikin 242 da ke jirgin suka mutu, mutum guda ne kawai ya tsira.
Masana na zargin cewa jirgin da zai kai fasinjoji birnin London ya yi hatsari ne sakamakon wani babban kuskure da ya faru yayin tashinsa.

Source: Getty Images
A sakamakon haka, an kafa cibiyoyin tallafi a filayen jirgin sama na Gatwick da ma wasu don taimakawa ‘yan uwan wadanda suka rasu, kamar yadda jaridar Financial Express ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuskuren da ya jawo hadarin jirgin AI171
A cewar wani kwararre kan fannin sufurin jiragen sama, Captain Steve, akwai yiwuwar direban jirgin ya tafka babban kuskure yayin tashin jirgin da ya jawo hadarin.
Ya bayyana cewa matukin jirgin na biyu ya bude na'urar fikafikan jirgi (flaps) maimakon ya dage tayoyin saukar jirgin, kuskuren da ya ce zai iya zama silar hadarin.
“Wannan na iya zama dalilin da zai sa jirgin ya daina tashi sama,”
- Inji Steve, yana mai cewa wannan kuskuren ya na janyo raguwar saurin iska da faɗuwar jirgi cikin gaggawa.
Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin hadarin ba
Jaridar Legit.ng ta lura cewa Captain Steve ya fadi ra'ayinsa ne kawai kan kuskuren matukin jirgin da ya ce ya jawo hadarin, domin ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan
Hare haren makiyaya: Abin da Tinubu ya fadawa gwamnan Benue da suka hadu a Aso Villa
Ana gudanar da bincike kan hadarin jirgi cikin tsari, kuma yakan dan dauki lokaci saboda hukumomin sufurin jiragen sama na bin keke-da-keke bisa dokokin kasa da kasa.
Ana fara binciken ne a wurin da hadarin ya faru, sannan a kammala shi da fitar da rahoton karshe a bainar jama’a da ke bayyana musabbabin hadarin jirgin da kuma matakan da aka dauka.
A bisa ka’idojin hukumar sufurin jiragen sama ta duniya (ICAO), ƙasar da hadarin ya faru ce ke jagorantar binciken, tare da hadin gwiwar kamfanin da ya kera jirgin, ƙasar, kamfanin jirgin ke ciki da sauran masu ruwa da tsaki.
A irin wannan babban hadari, ƙungiyoyi kamar NTSB ta Amurka ko BEA ta Faransa na iya turo ƙwararru don taimakawa, a cewar rahoton NTSB.
Abin da zai biyo bayan hadarin jirgin Air India
Masu bincike za su fara da kebe wurin hadarin da kuma tattara mahimman bayanai kamar: yadda sassan jirgin suka fado, rahoton yanayi, bayanan gyaran jiki da binciken kundin tashin jirgin.

Source: Twitter
Babban abu shi ne samun na’urorin da ke nadar sufurin jirgi (wanda aka fi sani da “black box”), waɗanda ke dauke da sauti daga cikin bangaren matuka da bayanan aikin jirgin, inji rahoton AP News.

Kara karanta wannan
Jirgin sama ya sake faduwa a kasar India, an rasa rayukan mutane 7 sun riga mu gidan gaskiya
Ana hada kwararru daga sassa daban-daban: injiniyan jirgin sama, masana halayen dan adam, da kuma masana yanayi, don tantance ababen da suka haifar da hadarin.
Sau tari bincike yakan nuna cewa ba abu guda daya tilo ne ke janyo hadari ba, akan samu dalilai da suka shafi: matsalar na’ura, kuskuren dan adam, munin yanayi, ko rashin sa-ido.
Bayan an gama rubuta rahoton farko, ana turawa bangarorin da abin ya shafa don su bada ra’ayinsu kafin a fitar da rahoto na ƙarshe, wanda ke bayyana abin da ya haddasa hadarin da kuma bada shawarwari na tsaro.
Maganar karshen matukin jirgin Air India
Tun da fari, mun ruwaito cewa, matuƙin jirgin Air India ya aika da saƙon gaggawa kafin hadarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 241 a Ahmedabad ranar Alhamis.
Kyaftin Sumeet Sabharwal ya aika wa tashar jirgin sako cikin firgici yana mai cewa, “Mayday… muna rasa ƙarfin jirgin, ba zai iya ci gaba da tashi ba,” bayan daƙiƙa 11 da tashi.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya rasa karfin da zai ɗaga shi sama, wanda a karshe ya fadi kan wasu gidaje, sannan ya kama da wuta, amma an ce mutum daya ya tsira.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
