Yaki Ya Barke tsakanin Rasha da Ukraine, Makami Mai Linzami Ya Kashe Mutane 15
- Rasha ta kai mummunan hari da makamai masu linzami kan Kyiv, inda ta kashe mutane 15 tare da raunata 156, a cewar Volodymyr Zelenskyy
- Harin ya ruguje wani gini mai hawa tara, wani tsohon gini na zamanin da a yammacin Kyiv, kuma ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru
- Shugaban Ukraine, Zelenskyy ya buƙaci kasashen duniya da su tsoma baki a lamarin, yayin da kira harin da "mafi muni" da Kyiv ta taba gani
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ukraine – Kasar Rasha ta kai mummunan hari da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan birnin Kyiv a safiyar Talata, inda ta kashe aƙalla mutane 15 tare da raunata 156.
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya kira harin da "ɗaya daga cikin munanan hare-hare" da aka kai Kyiv tun bayan barkewar yaƙinsu a 2022.

Source: Getty Images
Harin da Rasha ta kai Ukraine ya hallaka mutane
Ana tsoron adadin waɗanda suka mutu daga harin zai ƙaru, sakamakon makamai masu linzamin sun dura kan wurare da dama a faɗin birnin, a cewar rahoton The Guardian.
Wani gini mai hawa tara na zamanin Soviet da ke a yammacin Kyiv da wani makami mai linzami ya daka ya tarwatse, inda ya bar baraguzai masu yawa a yankin.
Akalla gidaje 30 da ke cikin ginin na Soviet ne suka lalace, in ji gwamnan Kyiv, Vitali Klitschko, yayin da yake duba wurin jim kaɗan bayan harin.
"Da yiwuwar akwai mutane a ƙarƙashin baraguzan, kuma ba za mu iya cire tsammanin cewa adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa ba."
- Vitali Klitschko.
Yayin da alfijir ya keto, ɗaruruwan ma'aikatan ceto suka fara ƙoƙarin janye baraguzan tare da kokarin ceto waɗanda suka makale a cikin wannan babban gini.
Makamin Rasha ya tarwatsa babban gini a Kyiv
An kuma rahoto cewa fashewar makami mai linzamin a wannan yanki ya shafi shaguna da wasu gine-gine, inda aka ce sun lalace a bangarori daban daban.
Ministan cikin gida, Ihor Klymenko, ya ce:
"Wani makami mai linzami ya kai sauka kai tsaye kan wani gini mai hawa tara, ya lalata wani sashi na ginin, kuma harin ya yi barna sosai."
An ji karar jirage marasa matuƙa a cikin dare, tare da sautin gargadin kai hari da ke aiki tsawon sa'o'i yayin da aka ce dubban mazauna Kyiv da suka nemi mafaka a tashoshin jirgin ƙasa.
Sautukan gargadin sun ci gaba da tashi a tsaknin gine-gine ne na duk faɗin birnin yayin da shigifan tsaron sararin samaniyar Kyiv ke ƙoƙarin kare hare-haren.

Source: Twitter
Martanin shugaban Ukraine kan harin Rasha
Zelenskyy ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:
"Kyiv ta fuskanci ɗaya daga cikin munanan hare-hare. Yanzu haka a Kyiv, ana ci gaba da ƙoƙarin ceto mutane daga ƙarƙashin baraguzai na wani gini, har yanzu ba a san yawan waɗanda suka makale ba."
Ya buƙaci ƙasashen duniya da kada su yi biris da abin da ke faruwa yayin da ce, "Putin yana yin haka ne kawai saboda yana ganin zai iya ci gaba da yaƙin. Burinsa shi ne a ci gaba da yaƙi."
Rasha ta shafe kusan kowane dare tana kai hari kan Ukraine tsawon shekaru uku na cikakken yaƙinsu, amma ba kasafai take kai hari kai tsaye kan Kyiv ba, saboda babban birnin yana da kariyar shigifan tsaron sama.
Kalli bidiyon harin a nan kasa:
"Rasha na shirin wargaza Ukraine" - Zelenskyy
Tun da fari, mun ruwaito cewa, kasar Rasha na shirin kai munanan hare-haren kare dangi kan kasar Ukraine, a cewar Shugaba Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine, Zelenskyy ya yi ikirarin cewa Rasha ta sayo sababbin makamai masu linzami daga Iran domin ci gaba da farmakar kasarsa.
A yayin da aka samu sassaucin yaki a tsakanin kasashen biyu, Zelenskyy ya ce ya samu bayanan sirri da suka nuna cewa Rasha na shirin ‘wargaza’ Ukraine a sabbin hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


