Rashin Tsaro: Shugaban Amurka, Trump Ya Samu Izinin Kakaba Takunkumi ga Najeriya

Rashin Tsaro: Shugaban Amurka, Trump Ya Samu Izinin Kakaba Takunkumi ga Najeriya

  • Majalisar dokokin Amurka ta ba Donald Trump damar sanya takunkumi kan Najeriya saboda kashe-kashe
  • Rahoto Amurka ya bayyana cewa Najeriya ce ke da kaso 90% na Kiristocin da ake kashewa a duniya duk shekara
  • Biyo bayan rahoton, an ji gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, tana mai cewa ba a yi wa kasar adalci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kwamitin Harkokin Kasashen Waje na Majalisar Wakilan Amurka ya amince da ba tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, damar sanya takunkumi ga Najeriya.

Kwamitin ya dauki wannan mataki ne biyo bayan wani zaman jin bahasi da aka gudanar, inda aka zargi gwamnatin Najeriya da kasa kare rayukan Kiristoci daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Amurka
Amurka na shirin kakaba wa Najeriya takunkumi. Hoto: Bayo Onanuga|Donald J.Trump
Asali: Facebook

Rahoton Arise News ya nuna cewa majalisar Amurka ta bukaci Donald Trump ya tattauna da shugaban Najeriya domin tabbatar da tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Sanata ya watsawa matasa kasa a ido, ya ki amincewa ya kara da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa ake son sa wa Najeriya takunkumi?

A cewar rahoton da aka gabatar, daga watan Oktoba 2019 zuwa Satumba 2023, an kashe mutane 55,910 yayin da wasu 21,000 suka shiga hannun ‘yan ta’adda a Najeriya.

Shugaban kwamitin da ke bincike kan lamarin, Chris Smith, ya ce halin da ake ciki a Najeriya yana bukatar daukar mataki cikin gaggawa.

Ya bayyana cewa shaidar da Bishop Wilfred Anagbe na cocin Makurdi ya bayar a zaman jin bahasin na da matukar muhimmanci.

Martanin Najeriya kan batun takunkumin

Tsohon Sanata Shehu Sani ya yi kakkausar suka kan wannan yunkuri na Amurka, yana mai cewa bai kamata a sanya wa Najeriya takunkumi ba.

A sakon da ya wallafa a X, Shehu Sani ya ce:

“Idan Amurka na da matsala da wasu mutane a Najeriya, to su dauki mataki a kansu kai tsaye. Da yawa daga cikinsu na da dukiyoyi da asusu a bankunan Amurka.”

Kara karanta wannan

Biyan haraji: Majalisa ta yi wa sojoji gata, an gabatar da muhimmin kudiri a gabanta

Shehu Sani
Tsohon Sanatan Najeriya, Shehu Sani a majalisa. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

A nata martanin, fadar shugaban kasa ta bakin mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ta ce gwamnatin Bola Tinubu na kokarin tabbatar da zaman lafiya.

Daniel Bwala ya kara da cewa shugaba Bola Tinubu ya mayar da hankali wajen fahimtar juna a tsakanin addinai.

Daniel Bwala ya wallafa a X cewa:

“Tun bayan hawar shugaban kasa Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023, babu wani rahoton nuna wariya ga Kiristoci a Najeriya.”

Bwala ya kara da cewa rahoton da kwamitin Amurka ya fitar bai dace da hakikanin yanayin da ake ciki ba, kuma ba a duba abubuwan da suka wakana a daidai lokacin da suka faru.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci Amurka da ta sake duba batun tare da fahimtar cewa Najeriya kasa ce da ke kokarin tabbatar da adalci ga kowa.

Kara karanta wannan

'Yar TikTok ta yi wani irin mutuwa mai ban tausayi, an samu gawarta a dakinta

An kama mutum 5 kan zargin sace sarki

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda a birnin tarayya Abuja ta cafke wasu mutane biyar da ake zargi da hannu wajen sace wani sarki.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun shiga har gida sun sace sarkin ne da tsakar dare tare da wasu mutane a lokacin da suka kai farmaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng