Jerin Mahajjatan Najeriya da Suka Rasu Yayin Aikin Hajjin 2024 da Jihohinsu

Jerin Mahajjatan Najeriya da Suka Rasu Yayin Aikin Hajjin 2024 da Jihohinsu

Mahajjatan Najeriya da dama sun rasa rayukansu yayin aikin Hajjin bana na shekarar 2024 da muke ciki a kasar Saudiyya.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Rahotannin sun ce aƙalla mutane fiye da 10 suka rasa rayukansu saboda zargin tsananin zafi yayin da wasu kuma rashin lafiya ya yi ajalinsu.

Cikakken sunayen alhazan Najeriya da suka rasu yayin aikin hajji
Hukumomi a Saudiyya sun tabbatar da rasuwar alhazan Najeriya da dama yayin aikin hajji. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Asali: Facebook

Legit Hausa ta binciko muku mahajjatan da hukumomi suka sanar sun mutu da kuma jihohinsu a Najeriya

Alhazan Najeriya da aka rasa a hajji

Jihar Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Hukumar alhazan Najeriya ta tabbatar da rasuwar Salman Mohammed daga Kwara a ranar 13 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Babban jami'in hukumar Kwastam ya mutu ana tsakiyar zaman kwamitin Majalisa

Marigayin ya rasu ne bayan ya fara rashin lafiya a Makkah inda ya ce ga garinku nan take.

2. Har ila yau, an sanar da rasuwar Hajiya Ayishat Shuaib Ologele a Saudiyya yayin da ta je aikin hajji.

Ayishat Shuaib Ologele ta rasa ranta ne yayin tafiya daga Makkah zuwa Madinah a ranar 13 ga watan Yunin 2024.

3. Ana fargabar Hajiya Hawawu Mohammed ta hallaka kanta a birnin Madina da ke kasar Saudiyyava ranar 9 ga watan Yunin 2024.

Hajiyar ta fito ne daga jihar Kwara inda hukumomin Saudiyya suka tabbatar da haka bayan gudanar da bincike.

4. Bayan rasuwar Hawawu Mohammed, hukumomin Saudiyya sun kuma tabbatar da rasuwar Saliu Mohammed.

Marigayin ya rasu ne yayin da yake karbar kulawa a sashin kula da mutane da ke cikin mummunan yanayi a Madinah.

Jihar Kebbi

Kara karanta wannan

Yadda kwankwaɗar kunun aya ya hallaka mutane 24, Gwamna ya dauki mataki mai tsauri

1. Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kebbi ta sanar da rasuwar Alhaji Abubakar Abdullahi a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Marigayin wanda ya fito daga kauyen Gulma a karamar hukumar Argungu ya rasu ranar 20 ga watan Yunin 2024.

2. An sanar da rasuwar Alhaji daga jihar Kebbi a Najeriya yayin da ya ke gudanar da aikin Hajji a kasa mai tsarki.

Marigayin mai suna Muhammad Suleiman ya rasu ne a ranar 27 ga watan Yunin 2024 bayan fama da jinya.

3. Hukumar alhazai a Najeriya ta sanar da mutuwar wata Hajiya daga jihar Kebbi a ranar 25 ga watan Yunin 2024.

Marigayiyar mai suna Tawalkatu Busare Alako ta rasu ne bayan ta yi fama da ƴar gajeruwar jinya.

Jihar Lagos

1. Hukumomi sun sanar da rasuwar Hajiya Ramota Bankole da ta yi fama da jinya kafin rasuwarta a ranar 20 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Ana cikin rigimar sarautar Kano, miyagu sun yi ta'asa har da jikkata yan sanda

Marigayiyar da jigo ce a jam'iyyar APC ta rasu a kasar yayin da ta je aikin hajjin bana.

2. Allah SWT ya karbi rayuwar ɗaya daga cikin alhazan jihar Legas mai suna Idris Oloshogbo.

Marigayin mai shekaru 68 a duniya ya rasu a ƙasa mai tsarki bayan fama da jinya a ranar 29 ga watan Yunin 2024.

Jihar Plateau

1. Hukumar alhazan Najeriya ta sana'ar da rasuwar wani Alhaji daga jihar Plateau mai suna Isma'il Musa.

Marigayin ya rasu a ƙasa mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajjin bana a ranar 19 ga watan Yunin 2024.

Jihar Niger

1. A ranar 8 ga watan Yunin 2024 aka sanar da rasuwar Ramatu Abubakar a ƙasa mai tsarki.

Hajiyar mai shekara 45 a duniya ta rasu ne a birnin Madinah na ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin bana.

Jihar Kaduna

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

1. Allah ya yi wa wata mahajjaciya daga jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Muhammad-Ladan rasuwa.

Hajiyar ta rasu ne a asibitin King Fahad da ke birnin Makkah a ranar Jumu'a 14 ga watan Yunin 2024 bayan fama da rashin lafiya.

Mai gadin Ka'abah ya rasu a Saudiyya

Kun ji cewa an shiga jimami bayan rasuwar mai gadin Ka'abah da ke kasar Saudiyya wanda ya shafe shekaru yana wannan aikin mai daraja.

Marigayin, Dakta Saleh Bin Zain Al-Shaibi ya rasu ne da safiyar ranar Asabar 22 ga watan Yunin 2024 inda aka sallar jana'izarsa nan take.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.