Hajj 2024: Bayan Mutuwar Tawakaltu, Wani Alhajin Najeriya Ya Mutu Yana Ibada a Saudiya

Hajj 2024: Bayan Mutuwar Tawakaltu, Wani Alhajin Najeriya Ya Mutu Yana Ibada a Saudiya

  • Wani Alhaji daga jihar Kebbi, Muhammad Suleman ya rasu bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a birnin Makka na kasar Saudiyya
  • Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi kuma an yi sallar jana’izarsa a masallacin Harami (Ka’aba) tare da yi masa sutura
  • Rasuwar Muhammad ta kara adadin yawan alhazan Najeriya da suka rasu zuwa biyu, bayan mutuwar Hajiya Tawakaltu Alako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Makkah, Saudiya - Wani Alhajin Najeriya da ke gudanar da aikin Hajji ya rasu a kasar Saudiyya, an ce marigayin dan asalin jihar Kebbi ne.

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, Faruku Aliyu-Enabo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: An shiga jimami bayan rasuwar maniyyaciya daga Arewa a Saudiyya

Dan Najeriya ya rasu wajen aikin Hajji a Saudiya
Wani dan jihar Kebbi ya rasu a Saudiya yayin da ya ke gudanar da aikin Hajji. Hoto: @MoHU_En
Asali: Twitter

Saudiya: Alhajin Najeriya ya rasu a Saudiya

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa marigayin Muhammad Suleman, ya rasu ne a ranar Lahadi bayan gajeruwar jinya a garin Makkah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan rasuwar wata Hajiya mai suna Tawakaltu Alako wadda ita ma ‘yar asalin jihar Kebbi ce.

Alako ta rasu ne a ranar Asabar bayan ta yanke jiki ta fadi otal din da ta ke zama a Makkah.

Aliyu-Enabo ya bayyana cewa an yi jana’izar Suleman kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, in ji rahoton jaridar The Cable.

Gwamnatin Kebbi ta mika sakon ta'aziyya

“Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma an yi sallar jana’izarsa a masallacin Harami (Ka’aba).
“A madadin gwamnatin jihar Kebbi, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa, alhazan Kebbi da daukacin jihar baki daya.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: An shiga jimami yayin da ɗan Majalisa mai-ci ya rasu a Adamawa

"Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma jikansa da rayukan dukkan Musulmin da suka rasu."

- Faruku Aliyu-Enabo.

An nada Amirul Hajji na Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya nada sabon Amirul Hajji da zai jagoranci maniyyatan Kano zuwa aikin Hajjin bana a Saudiya.

Abba ya nada mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam a matsayin Amirul Hajj na Kano a bana yayin da alhazan jihar za samu kyautar $500 kowannensu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.