Rai Bakon Duniya: Wani Alhaji Daga Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Saudiyya

Rai Bakon Duniya: Wani Alhaji Daga Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Saudiyya

  • An sake samun wani Alhaji wanda ya fito daga jihar Plateau da ya riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024
  • Alhajin mai suna Ismaila Musa ya rasu ne bayan ya shafe kusan makonni uku yana jinya a asibitin ƙwararru da ke birnin Makkah na ƙasar Saudiyya
  • Hukumar jin daɗin Alhazan jihar Plateau wacce ta tabbatar da rasuwar marigayin a cikin wata sanarwa, ta yi ta'aziyyar rasuwarsa ga iyalansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Wani Alhaji da ya fito daga jihar Plateau, ya riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki wajen gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Sakataren hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar, Alhaji Hayabu Dauda, ya tabbatar da rasuwar Alhajin mai suna Ismaila Musa, a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: An samu wani Alhaji 'dan Najeriya ya sake rasuwa a Saudiyya

Alhaji daga Plateau ya rasu a Makkah
Alhaji daga jihar Plateau ya rasu a Saudiyya Hoto: Haramain
Asali: Facebook

Alhaji daga Plateau ya rasu a Saudiyya

Alhaji Hayabu Dauda ya bayyana cewa Alhajin ya rasu ne a asibitin ƙwararru na Annur da ke birnin Makkah, inda ya shafe makonni uku yana jinya, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar PM News ta ce a cikin wata sanarwa da sakataren hukumar ya rabawa manema labarai a birnin Jos a ranar Talata, hukumar ta yiwa iyalan marigayin ta'aziyyar rasuwarsa.

Hukumomi sun yi ta'aziyyar rasa Alhaji

"Ya yi rashin lafiya inda aka kwantar da shi a asibitin ƙwararru na Annur a Makkah tun ranar, 31 ga watan Mayun 2024."
"Muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyalansa, gwamnati da al’ummar Jihar Plateau tare da yi masa addu’ar Allah ya karɓi aikin Hajjinsa, ya kuma ba shi hutu na har abada."

- Alhaji Hayabu Dauda

Sakataren ya yi addu’ar Allah ya ba iyalansa haƙuri da juriya wajen jure wannan babban rashin da suka yi.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da sojan Najeriya ya salwantar da ransa

Alhaji Ismaila Musa ya fito ne daga ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Alhazan Najeriya sun rasu a Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu rasuwar ƙarin mahajjata guda biyu a ƙasar mai tsarki yayin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.

Mahajjatan biyu sun fito ne daga jihar Kwara da aka bayyana da Salman Muhammad Alade da kuma Ayishat Shuaib Ologele.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng