Innalillahi, Allah Ya Yiwa Wata Hajiya Daga Jihar Kaduna Rasuwa a Ƙasa Mai Tsarki

Innalillahi, Allah Ya Yiwa Wata Hajiya Daga Jihar Kaduna Rasuwa a Ƙasa Mai Tsarki

  • Wata mahajjaciya daga jihar Kaduna, Hajiya Asma'u Muhammad Ladan ta riga mu gidan gaskiya a ƙasar Saudiyya ranar Jumu'a, 15 ga watan Yuni
  • Mai magana da yawun hukumar alhazai ta jihar Kaduna, Malam Yunusa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar hawan Arafah
  • Ya ce tuni hukumar ta sanar da ƴan uwan marigayyar kuma ta musu ta'aziyya tare da addu'ar Allah ya gafarta mata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Arabia - Allah ya yi wa wata mahajjaciya daga jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Muhammad-Ladan rasuwa a kasa mai tsarki.

Hajiya Asma'u ta rasu ne a asibitin King Fahad da ke birnin Makkah a Saudi Arabia ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuni bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Hajji 2024: Manyan abubuwan da huɗubar Arafa ta mayar da hankali a kai

Alhazai a Ka'abah.
Najeriya ta kara rasa Hajiya yar jihar Kaduna a ƙasa mai tsarki Hoto: Inside The Haramain
Asali: Getty Images

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna, Malam Yunusa Muhammad-Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar hawan Arafah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwar da ya rabawa manema labarai yau Asabar, Malam Yunusa bai bayyana sunan ƙaramar hukumar da marigayyar ta hito ba, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa Hajiya Asma'u ta yi rijista a hedkwatar hukumar alhazan kafin Allah ya karɓi rayuwarta.

Hukumar alhazai ta yi ta'aziyya

Haka nan kuma mai magana da yawun hukumar alhazan Kaduna ya sanar da cewa tuni aka tura saƙon rasuwarta ga iyalanta.

Ya kara da cewa, mahukunta da ma’aikatan hukumar sun jajanta musu bisa rasuwar Hajiya Asma’u, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

A cewar Muhamamda-Abdllajhi, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta yi addu’ar Allah SWT ya jikan marigayiyar, ya gafarta mata kuma ya bai wa iyalanta haƙuri.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sauratar Kano, fitaccen basarake ya mutu a Arewa

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da alhazai sama da miliyan 1.5 ke hawan Arafah, ɗaya daga cikin ranaku masu muhimmanci da falala a addinin Musulunci.

Za a fassara huɗubar Arafah

A wani rahoton kuma hukumar kula da Masallatai masu alfarma a ƙasa mai tsarki ta ce za a fassara hudubar hawan Arfah zuwa harshen Hausa da wasu harsuna 19.

Alhazai sama da miliyan 1.5 ne za su taru a filin Arafah ranar Asabar, 16 ga watan Yuni cikinsu har da Musulmi 65,000 daga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262