'Yan Sanda sun Kama 'Yan Najeriya Masu Yaudarar Mata da Soyayyar Karya a Turai
- Yan sandan kasar Jamus sun bayyana cewa sun damke wasu mutane 11 bisa zargin aikata zamba a soyayya tare da yaudarar yan kasar
- Rundunar yan sandan kasar ta ce dukkanin wadanda ta kama na dauke da shaidar dan kasa ta Najeriya, kuma sun dade su na cin karensu ba babbaka
- Rahotanni sun ce akalla, rahoto 450 na zambar soyayya aka gano a shekarar 2023 kadai, yayin da kwararrun masu wasa da zuciyar su ka ci $5.7 miliyan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Germany- Wasu kwararrun yan zambar soyayya 11 yan asalin Najeriya sun shiga komar yan sandan kasar Jamus.
Kwararrun masu wasa da zuciya da sunan soyayya na gudanar da hada-hadarsu karkashin kungiyar Black axe.
A wata sanarwa da yan sandan Bolivia su ka fitar, sun ce zambar soyayya na daga hanyoyin da ake auren yan kasar da niyyar zambatarsu, kamar yadda Channels Television ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Black axe na da karfi," Yan sanda
Rundunar yan sandan Jamus ta ce yan kungiyar Black axe na da karfin fada a ji a siyasar Najeriya da gudanarwar kasar.
Sun ce yan kungiyar kan yi aure a Jamus, sai su fara tatike wadanda su ka aura, wasu lokutan da sunan kawo tallafi Najeriya karkashin kungiyar Neo Black Movement of Africa.
Vanguard News ta ruwaito cewa akalla an samu rahotonni 450 na wadanda su ka damfari mazauna Bavaria da sunan soyayya a shekarar 2023 kadai, tare da awon gaba da kudi $5.7 miliyan zuwa Najeriya.
Rundunar yan sandan ta ce dukkanin wadanda ake zargi na cikin kungiyar Black axe na rike da takardar shaidar yan Najeriya kuma shekarunsu na tsakanin 29 zuwa 53.
An rufe asusun a Amurka saboda zamba
A baya mun kawo mu ku yadda kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta rufe asusunta bayan samun rahoton wasu daga mambobinta na aikata zamba.
Asusun da ke Amurka dai, an bude shi ne domin karbar kudin wata-wata daga yan kungiyar, amma sai bankin ajiyar ya ce wasu na aikata zamba da shi.
Asali: Legit.ng