An Rufe Asusun Ajiyar Banki Na IPOB a Amurka Saboda 'Zamba'

An Rufe Asusun Ajiyar Banki Na IPOB a Amurka Saboda 'Zamba'

  • Wata banki a kasar Amurka ta rufe asusun ajiyar kudi na kungiyar masu son kafa Biafra, IPOB
  • Bankin ta rufe asusun ne bayan an yi zargin ana aikata abubuwa masu alaka da zamba da asusun
  • Sai dai kungiyar ta IPOB ta sake bude wani asusun bankin da za ta rika amfani da shi wurin karbar kudaden wata-wata daga mambobinta

Kungiyar masu faftikar kafa kasar Biafra, IPOB, ta ce ta rufe assusun ajiyan kudi a bankinta da ke kasar Amurka, a cewar rahoton The Cable.

Sanarwar da Chika Edoziem, shugaba a kungiyar ta IPOB, ya fitar a ranar Alhamis ta ce ana amfani da asusun ajiyar ne domin karbar kudaden da mambobin IPOB ke biya duk wata.

An Rufe Asusun Ajiyar Banki Na IPOB a Amurka Saboda 'Zamba'
Mambobin haramtaciyyar kungiyar IPOB. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Edoziem ya ce IPOB ta rufe asusun ajiyar bayan ta samu rahoto daga bankin na cewa wasu mutane da ba a bayyana ko su wanene ba suka zargin ana aikata zamba da asusun ajiyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta ce maza su hakura kawai, a mika wa mata ragamar Najeriya

Ya ce an bude wani sabon asusun ajiyar banki da mambobin za su cigaba da biyan kudadensu na wata, yana mai shawartarsu da su yi biyaya ga sabon umurnin.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban kungiyar IPOB na duniya baki daya, Nnamdi Kanu, ya bada umurnin bude sabon asusun ajiyar banki na IPOB a Amurka, an umurtar mambobi su cigaba da biya kudadensu na wata.
"Wannan asusun ta Amurka itace asusun da shugaban mu ya ce a rika tura kudin tallafi na ESN.
"Sakamakon rahoton da wasu da ba a san ko su wanene ba suka tura wa bankin na alakanta asusun da zamba, banki ta bukaci a rufe asusun."

Kotun tarayya da ke zamansa a Abuja, a 2017 ya ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci kuma aka haramta ayyukanta.

Ana zargin shugabanta Nnamdi Kanu da laifuka masu alaka da cin amanar kasa bisa yunkurinsa na kafa Jamhuriyar Biafra.

Yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS, yana jiran lokacin da kotu za ta cigaba da shari'arsa a ranar 26 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164