Gaza: Bam Ya Kashe ‘Yanuwa 36 Lokacin Shirin Sahur a Dauki Azumin Ramadan
- Ana zargin cewa sojojin kasar Israila sun bude wuta inda suka hallaka mutanen Gaza da ke zaune a wani gida a sansanin Nuseirat
- Rahotanni sun nuna watakila gwamnatin Israila ta yi umarni a kai harin da ya yi sanadiyyar mutanen mutanen da ke cikin kangi
- Tun a watan Oktoban bara ake kashe mutanen Falasdina a matsayin ramuwar gayyan harin da ‘yan kungiyar Hamas suka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Gaza - Bayan sojojin Israila sun tarwatsa su, mutane daga dangin Tabatibi a Falasdin sun tare a tsakiyar Gaza, amma ba su tsira ba.
Rahoton da aka samu daga tashar Aljazeera ya tabbatar da cewa an kai wani hari ta sama da ya kashe wadannan mutane a Gaza.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ambasada Bawa ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, bayanai sun fito
A yayin da Bayin Allah suke shirin yin sahur a ranar Juma’a, sai aka yi masu luguden wutar da tayi sanadiyyar kashe su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon tarwatsa gidan da dangin suke rabe, mutane 36 aka rahoto cewa sun mutu a wannan sansani da yake a Nuseirat.
Gaza: Gwamnati tace an kashe mutum 36
Ma’aikatar kiwon lafiya da ke Gaza ta tabbatar da wannan adadi, ta kuma zargi kasar Israila da kai wannan mugun hari a Nuseirat.
Jaridar Middle East Monitor ta rahoto cewa wani mutumi ya daina magana kuma ya manta komai bayan an kashe masa 'yanuwa.
An kashe Bayin Allah a Gaza da Ramadan
Wani Mohammed al-Tabatibi mai shekara 19 wanda ya samu rauni a hannu ya bayyana cewa ya rasa mahaifi da mahafiyarsa.
“Wannan uwa ta ce, wannan uba na ne, wannan kuwa goggo na, wadannan ‘yanuwa na ne.
Sun tarwatsa gidan yayin da mu ke ciki. Mahafiyata da goggo na suna kokarin shirya abincin sahur.
Dukkansu sun yi shahada.”
- Mohammed al-Tabatibi
Wannan matashi ya yi magana ne yayin da gawawwakin ke asibitin Al-Aqsa a Deir al-Balah, daga nan aka kai su makabarta.
An kashe ladadin masallaci a Gaza
Saboda karancin kayan aiki da kuma irin yadda aka yi barnar, tashar RFI tace ba a iya ceto duka wadanda aka kashe a harin ba.
Mahmoud Duhair ya ce an kashe ladadin masallacinsu, wani Issa Duhair mai shekara 41, ya je yin sahur kenan sai aka sa bam.
Jami’ar yada labarai ta gwamnatin Hamas, Salama Maarouf tayi Allah wadai da harin. Ana tsoron adacin mamatan zai iya zarce 36.
Sojojin Israila sun ce ana duba lamarin, yanzu dai sun kashe mutane kusan 32, 000.
Kashe-kashe a Arewacin Najeriya
Idan aka dawo Najeriya, za a ji labari kwanaki wani Magaji Lawal ya mutu a hannun Askarawa a wani yanayi mai alamar tambaya.
A wata budaddiyar wasika da aka rubuta, ana so gwamnatin Zamfara ta binciki aikin Askarawan jihar yayin da zargi ya fara yawa.
Duk da haka, an yaba da gwamnatin Dauda Lawal ta kawo jami’ai 2, 645 da za su yaki ‘yan bindigan da suka addabi jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng