Yadda Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso Daga ECOWAS Zai Kawo Matsaloli a Afrika

Yadda Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso Daga ECOWAS Zai Kawo Matsaloli a Afrika

  • Burkina Faso, Mali da Nijar sun fita daga kungiyar ECOWAS da aka yi shekaru kusan 50 ana tare
  • Masana sun ce sauyin da aka samu a wannan kungiya mai tasiri yana da hadari ga yankin Afrikan
  • Za a samu tawayar tattalin arziki saboda raguwar kasuwanci da kuma yiwuwar karin matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ficewar Burkina Faso, Mali da Jamhuriyyar Nijar daga karkashin kungiyar ECOWAS yana da mummunan tasirin tattali.

Rahoton da aka samu daga Punch yace matakin zai nakasa kasuwancin kasashen yammacin Afrika da ya kai Dala biliyan 277.22.

ECOWAS
Shugaban ECOWAS Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Cinikin ECOWAS zai ragu a Afrika

Cinikin kayan da ake yi a duk shekara tsakanin kasashen da ke yankin yammacin nahiyar Afrikan ya zarce fam Dala biliyan 270 a yau.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike: Ana kukan tsadar rayuwa, Minista yayi karin kudin makarantu a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka alkaluman da aka samu daga shafin ECOTIS suka tabbatar a 2022, babu tabbacin ko cinikin ya karu daga lokacin zuwa yanzu.

Babban cibiyar kasuwanci na duniyar ta kan bibiyi cinikin da kasashe suke yi duk shekara. Atiku Abubakar ya yi tsokaci a kan batun.

ITC tana aiki ne da majalisar dinkin duniya da kungiyar WTO da Ngozi Okonjo-Iweala a yanzu, tana samun bayanai daga COMTRADE.

Masana sun yi fashin baki a kan halin ECOWAS

Masana sun shaidawa Daily Trust cewa rashin hulda da Mali, Burkina Faso da Nijar zai kawo tasgaro ta fuskar kasuwanci da tattali.

Yanke alaka da ECOWAS yana da mummunan tasiri da fuskar matsalar tsaro a Afrika musamman idan aka duba yanayin yankin Mali.

Farfesa Jibril Ibrahim ya bayyana cewa kungiyar ECOWAS da wadannan kasashe za su ga tasirin wannan matak nan da wani lokaci.

Kara karanta wannan

Dala ta lula zuwa N1400, CBN ya dauki matakin kubutar da ragowar darajar Naira

Masana sun ce ba a taba ganin alaka ta tabarbare haka ba tun 1975. Ana zargin matakin da Bola Tinubu ya dauka ba su taimaka ba.

Juyin mulki sun raba kan ECOWAS

Idan aka tafi a haka, kasuwancin da ake yi da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar zai ragu a sakamakon juyin mulki da aka shirya.

Sojoji sun kifar da gwamnatocin da ke mulki a wadannan kasashe uku na Afrika.

Hambarar da gwamnatin farar hula ya jawo ECOWAS ta dakatar da kasashen daga 2021 zuwa 2023, yanzu sun zabi su fice gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng