El-Zakzaky Ya Zargi Amurka, Faransa Da Hura Wutar Rikicin Najeriya Da Nijar Don Kawo Rudani

El-Zakzaky Ya Zargi Amurka, Faransa Da Hura Wutar Rikicin Najeriya Da Nijar Don Kawo Rudani

  • Jagoran kungiyar Shi'a a Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky ya zargi Faransa da Amurka wurin kara hura wutar rikici tsakanin Najeriya da Nijar
  • El-Zakzaky ya bayyana haka ne yayin da ya ke wa'azi ga dalibansa a gidansa da ke birnin Tarayyar Nigeria, Abuja
  • Ya ce wannan fadan bai shafi kasar Najeriya ba tunda an yi juyin mulki da dama a kasar amma babu wanda ya zo ya ce zai dawo da dimukradiyya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban mabiya Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya zargi Amurka da Faransa kan hura rikici tsakanin Najeriya da Nijar.

El-Zakzaky ya ce ba irin munafircin da Turawa ba su sani ba wurin haddasa yaki idan su ka ga dama.

El-Zakzaky ya gargadi 'yan Najeriya kan rikicin Nijar
El-Zakzaky Ya Yi Martani Kan Rikicin Najeriya Da Nijar Bayan Juyin Mulki. Hoto: Legit.ng.
Asali: UGC

Ya ce za su iya kai farmaki a wata kasa da ke gaba da wata don wacce aka kai wa farmakin da dauka dayar ce ta kai musu hari.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

Shugaban Shi'a ya bayyana haka ne lokacin da ya ke wa'azi ga dalibansa a gidansa da ke Abuja, Aminiya ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Duk juyin mulkin da aka yi a Najeriya wata kasa ta taba zuwa ta tilasta bin farar hula?, sau nawa aka yi juyin mulki a Najeriya?.
"A wane dalili za ka dauki makami ka mamaye kasa da sunan dimokradiyya?.
"A bayyana ya ke wannan ba yakin mu ba ne, yaki ne tsakanin Faransa da Amurka duk da cewa Faransa na shawagi a sararin samaniyar Nijar bayan ta kulle."

Ya ce kasashen na amfani da 'yan ta'addan Boko Haram don kai wa mutane hari, su kuma su kwashe ma'adinan kasar, cewar Leadership.

Ya kara da cewa:

"Ina fargabar za su yi amfani da wadannan 'yan ta'addan wurin kai farmaki kasashen biyu don jawo husuma.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Hakura Da Biliyan 300 Da Za Ta Gada Don Auren Masoyinta Bakin Fata, Iyayenta Sun Yafewa Duniya Ita

"Za su iya haddasa fadan kabilanci tsakanin Najeriya da Nijar ta hanyar fakewa da hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum."

'Yan Shi'a Na Zanga-Zanga A Kaduna

A wani labarin, Kungiyar 'yan Shi'a a jihar Kaduna sun fara zanga-zanga tare da cika titunan birnin.

Kungiyar ta cika titunan birnin ne don nuna rashin jin dadinsu kan rashin adalci da ake nuna wa shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Asali: Legit.ng

Online view pixel