Shugaba Tinubu Ya Sanar Cewa 'Yan Najeriya 12m Za Su Rika Samun N8,000 Kowane Wata

Shugaba Tinubu Ya Sanar Cewa 'Yan Najeriya 12m Za Su Rika Samun N8,000 Kowane Wata

  • Majalisar wakilai ta karɓi wasiƙa daga wajen Shugaba Tinubu kan cewa zai riƙa biyan ƴan Najeriya wasu kuɗaɗe a kowane wata
  • Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta riƙa tura N8,000 a kowane wata ga talakawa mutum miliyan 12
  • Waɗannan talakawan waɗanda za a zaɓo daga jihohin ƙasar nan 36, za su riƙa samun kuɗaɗen ne har na tsawon wata shida

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa talakawa mutum miliya 12 za su riƙa samun N8,000 kowane wata har na tsawon wata shida domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

A cikin wata wasiƙa zuwa ga majalisar wakilan wacce kakakinta Abbas Tajudeen ya karanto a zaman majalisar na ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, Tinubu ya ce za a biya kuɗin ne domin rage raɗaɗin da talakawa ke ciki, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jiga-Jigai a Villa, Ya Faɗi Yadda Ya Zama Shugaban ECOWAS

Shugaba Tinubu zai ba talakawa tallafi
Tinubu ya ce 'yan Najeriya miliyan 60 za su amfana da shirin Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu zai taimaki talakawa da gajiyayyun ƴan Najeriya

Shugaban ƙasar ya aike da wasiƙar ne domin neman amincewar majalisar samo ƙarin kuɗaɗen da za a gudanar da shirin walwala da jindaɗi na ƙasa wanda majalisar ta kawo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa biyan kuɗin zai sanya ƴan Najeriya mutum miliyan 60 su amfani da shirin.

Domin tabbatar da sahihancin biyan kuɗin, shugaban ƙasar ya ce za a riƙa tura kuɗaɗen ne kai tsaye zuwa asusun waɗanda za su amfana da shirin.

Ƴan Najeriya sun yi martani

Wasu ƴan Najeriya sun garzaya soshiyal midiya domin bayyana ra'ayoyinsu akan wannan sabon shirin na shugaba Tinubu.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikinsu daga manhajar Twitter. Ga wasu daga ciki a nan ƙasa:

@Asiwaju__Aso ya rubuta:

"Wannan ci baya ne, ba cikin yanayi na yaƙi mu ke ba. A siyo motoci domin jigilar mutane kyauta sannan a samar musu da ruwa da lantarki a gidajensu, a cire kowane haraji kan magungunan yara, a inganta asibitoci. Haka ake rage raɗaɗin da talakawa ke ciki."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar Labour Ta Nemi a Tsige Shugaban INEC a Kuma Gudanar Da Bincike a Kansa, Ta Ba Da Dalili

@TonexBat23 ya rubuta:

"Sam bana goyon bayan irin wannan tallafin saboda magana ake kan ƴan Najeriya gaba ɗaya ba wasu ƴan Najeriya mutum miliyan 12 ba."

@usmanolatunji3 ya rubuta

"Ina adawa da hakan. Shirme ne wannan."

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ma'aikacin gwamnati mai suna Injiniya Buhari Hussain, wanda ya bayyana ra'ayinsa dangane da wannan tallafin da za a bayar.

A cewarsa tallafin N8,000 da ake shirin bayarwa ya yi kaɗan domin ko ƙishi ba zai gusarwa da waɗanda za a ba tallafin, inda ya ce za a lasa musu zuma ne a baki kawai.

Ya bayar da shawarar cewa kamata yayi ace kuɗin su kai mafi ƙarancin albashin da ake biya a ƙasar nan, sannan idan an bada hakan sai a rage yawan mutanen da aka tsara tunda farko za a tallafin.

Shugaba Tinubu Zai Ciyo Bashin Dala Miliyan 800

A wani labarin kuma, shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawa domin ya ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya.

Kara karanta wannan

Shugaban Tinubu Ya Ayyana Ta Ɓaci Kan Batun Samar da Abinci a Najeriya, Ya Bada Sabon Umarni

Shugaban ƙasar zai ciyo bashin ne domin tallafawa ƴan Najeriya masu rauni da ƙarancin abun hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng