Kamar Najeriya, Wata Kasar Afrika Ta Sanar Da Rage Tallafin Man Fetur, Ta Bayar Da Dalilanta

Kamar Najeriya, Wata Kasar Afrika Ta Sanar Da Rage Tallafin Man Fetur, Ta Bayar Da Dalilanta

  • Ƙasar Angola ta yanke shawarar bin sahun Najeriya wajen rage yawan kuɗaɗen da take kashewa a kan tallafin man fetur
  • Farashin man fetur zai ƙaru daga kwanza 160 (kuɗin ƙasar) zuwa kwanza 300 (kuɗin Angola) a kowace lita, wanda ke nuni da ƙaruwar farashin da kaso 87.5 cikin dari
  • Manuel Junior, ƙaramin ministan tattalin arziƙin ƙasar, ya ce hakan ba zai shafi tallafin da ake bayarwa kan sauran kayayyaki irin su dizal, man girki, da makamantansu ba

Ba iya Najeriya ba ne kadai ake fama da batun tallafin mai, domin kuwa kasar Angola ta sanar da cewa ta yanke shawarar rage kuɗaɗen da take kashewa kan tallafin man fetur, kamar yadda ya zo a wani rahoto da Bloomberg ta fitar.

Bayan taron majalisar ministocin ƙasar a ranar Alhamis a Luanda babban birnin ƙasar, Manuel Junior, karamin ministan kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasar, ya ce rage tallafin zai fara aiki daga ranar Juma'ar nan.

Kara karanta wannan

Iyaye Sun Bayyana Yadda Wasu ’Yan Banga Suka Lakadawa Dansu Duka Har Lahira a Kano

Wata kasa ta bi sahun Najeriya wajen rage tallafin mai
Angola ta rage kudaden da take kashewa a tallafin mai. Hoto: Africa News
Asali: UGC

Farashin zai karu da kaso 87.5 cikin 100

Ya ce hakan zai haifar da karin farashin man fetur daga kwanza 160 (kimanin $0.27) a kowace lita, zuwa kwanza 300 (kimanin $0.51) a kowace lita, kamar yadda The Cable ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce sauyin farashin na nufin an samu ƙaruwar farashin da kashi 87.5 cikin ɗari. Daga ƙarfe ɗaya na daren Juma'a dokar za ta fara aiki.

Sai dai ya ce hakan ba zai shafi tallafin da ake bai wa sauran albarkatun ƙasa ba, irin su dizal, man girki, da wani nau'i daban na dizal.

Ministan ya ce cire tallafin man fetur ɗin mataki ne da ya dace don inganta ci gaban tattalin arziƙi, wanda zai iya magance matsalolin da ke addabar ƙasar.

Angola na kashe kuɗaɗe da yawa wajen bayar da tallafin man fetur

Kara karanta wannan

Manajan NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Junior ya ce kuɗaɗen da Angola ta kashe kan tallafin mai ya kai dala biliyan uku da digo takwas ($3.8) a shekarar 2022.

A nata ɓangaren, ministar kuɗi ta Angola, Vera Daves, ta ce cire tallafin man fetur ɗin wani mataki ne na gwamnatin Angola, kuma ba ya da tasiri daga waje, wato daga asusun ba da lamuni na duniya (IMF).

A cewar rahoton gwamnati da Xinhua ta samu, ma'aikatar kuɗi ta ƙasar Angola ce ta gabatar da shawarar rage tallafin man fetur ɗin da suke son ya fara aiki a zango na biyu bisa huɗu na shekarar 2023.

Rahoton ya kuma ba da shawarar cewa a bi sannu a hankali a cire tallafin man dizal da sauran albarkatu, sannan a kuma ci gaba da aiwatar da hakan har zuwa shekarar 2025.

Angola ce kasa ta huɗu a arhar mai a duniya

Angola ce ƙasa ta huɗu mafi arhar man fetur a duniya ($0.28) bayan Libya, Iran, da Venezuela, a cewar bayanai da Globalpetrolprices.com ta tattaro.

Kara karanta wannan

Arzikin Dangote Ya Yi Tashin Gwauron Zabi, Ya Koma Cikin Jerin Hamshakan Attajirai 70 a Duniya

A cewar wani rahoto da ƙungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) ta fitar a ranar 11 ga watan Mayu, Angola ita ce kan gaba wajen samar da danyen mai a nahiyar Afirka, inda ake hako ganga miliyan 1.06 a kowace rana a watan Afrilu.

Mele Kyari ya bayyana dalilin da ya sa dole a cire tallafin man fetur

A wani labarin da muka wallafa a baya, babban daraktan kamfanin mai na ƙasa (NNPC) Mele Kyari ya bayyana cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta cire tallafin da take bayarwa na man fetur da ake shigowa da shi.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta iya ci gaba da biyan waɗannan maƙudan kuɗaɗe ba da ake biya na tallafin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel