Jirgin Rundunar Sojin Kasar Nijar Ya Yi Hatsari, An Rasa Rayuka Uku

Jirgin Rundunar Sojin Kasar Nijar Ya Yi Hatsari, An Rasa Rayuka Uku

  • Jirgin Helikwafta na rundunar sojin sama a kasar Nijar ya yi hatsari yayin da yake kokarin sauka a filin jirgin Niamey
  • Ma'aikatar tsaron kasar tace lamarin ya faru ne ranar Litinin 26 ga watan Disamba, 2022 bayan ya dawo daga shawagin ba da horo
  • Mutane uku dake cikin jirgin sun mutu nan take, Nijar na fama matsalar masu ikirarin jihadi a kudancin kasar

Jirgi mai saukar Angulu na rundunar sojojin kasar Nijar ya yi hatsari yayin da yake kokarin sauka a sansanin soji na filin jirgin Niamey ranar Litinin 26 ga watan Disamba, 2022.

Jaridar Vanguard ta ce ma'aikatar tsaro ta ƙasar Nijar ce ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.

Hatsarin jirgin sama.
Jirgin Rundunar Sojin Kasar Nijar Ya Yi Hatsari, An Rasa Rayuka Uku Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ma'aikatar tsaron ta ce haɗarin ya faru ne lokacin da jirgin Helikwaftan kirar ƙasar Rasha Mi-17 chopper ya dawo daga shawagin ɗaukar horo.

Kara karanta wannan

Matsanancin Halin Talaucin da za ka bar mu Ciki ya fi Wanda ka Tarar da mu, Kukah ga Buhari

Sanarwan ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bisa rashin sa'a dukka mutane ukun dake ciki, Sojan Nijar, NCO da mai koyarwa ɗan ƙasar waje, sun mutu nan take duk da namijin kokarin hukumomin agaji na kashe wutar da ta kama."

Sanarwan ta kara da cewa tuni ma'aikatar ta kaddamar da bincike don gano musabbabin abin da ya jawo wannan hatsarin.

Ƙasar Nijar mai maƙwaftaka da Najeriya itace kasar da tafi kowace talauci a cewar rahoton United Nations Human Development Index (HDI).

Kamar dai Najeriya, kasar Nijar na fama da matsalar rashin tsaro, wanda sakamakon haka ta ci gaba da ba Sojoji horo domin su fuskanci masu ikirarin jihadi a kudu maso yamma da kudu maso gabashin ƙasar.

Nijar na samun taimakon horo da kayan aiki daga ƙasar Faransa da kuma Amurka, waɗan da ke da sansanin sojin sama a Nijar. Haka tana samun taimako daga Belgium da Italiya.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindiga a Kaduna, Sun Kwato Bindigogin AK47 Guda 4

A wata sanarwan ta daban Ma'aikatar tsaro tace luguden wuta ta sama ya sheke yan ta'adda 25 a yammacin yankin Tillaberi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Hadimin Gwamnan Jam'iyyar APC Ya Mutu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma Allah ya yi wa ɗaya daga cikin hadiman gwamna Ebonyi sakamakon hatsarin mota ranar Kirsimeti

Hadimin gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, Mista Sunday Agwu, ya rasu sakamakon hatsarin motan da ya rutsa da shi. Tuni dai kusoshin siyasa suka fara aike wa da sakon ta'aziyya ga iyalansu, waɗanda murnar zuwan kirsimeti ta koma juyayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel