Ka Sake Tabarbara Kasar Fiye da Yadda ka Same ta, Kukah ga Buhari

Ka Sake Tabarbara Kasar Fiye da Yadda ka Same ta, Kukah ga Buhari

  • Babban faston majami'ar Katolika na Sakkwato, Fasto Matthew Hassan-Kukah ya bayyana takaicinsa game da yadda masu mulki ke son maida kasar filin daga
  • A cewarsa, duk da irin manyan alkawuran da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi 'yan Najeriya, gashi nan yana kokarin barin talakawa a matsanancin talauci da yafi na da
  • Ya kara da cewa, baya ko tantama, Buhari yafi samun ingantacciyar lafiya fiye da kafin ya hau mulki, amma 'yan Najeriya basu mora daga tagomashin lafiyarsa ba

Babban faston majami'ar yankin Katolika na Sakkwato, Matthew Hassan-Kukah ya ce duk da irin manyan alkawura da dama da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, a yanzu zai bar 'yan Najeriya "a matsanancin talauci" fiye da lokacin da ya amshi mulki a 29 ga watan Mayu, 2015.

Kara karanta wannan

Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000

Hassan Kukah
Ka Sake Tabarbara Kasar Fiye da Yadda ka Same ta, Kukah ga Buhari. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Fusataccen malamin addinin ya kara da cewa baya ko tantama lafiyar Buhari ta karu a tsawon shekaru bakwai da rabi da suka shude amma yaso a ce miliyoyin 'yan Najeriya sun mori tagomashi daga ingantacciyar lafiyar da Buhari ya samu ta hanya damar samun ingantacciyar kulawa ta lafiya a kasar.

Dattijon malamin mai da'awa ya fadi hakan ne a sakon Kirsimetinsa na shekarar 2022, mai taken, 'Najeriya: Bari mu bude sabon shafi' wanda ya gabatarwa Daraktan sadarwa na Channels TV, Rabaran Christopher Omotosho.

"Mai girma shugaban kasa, ina taya ka da iyalinka murnar Kirsimeti. Ina magana ne a madadi na da sauran 'yan Najeriya idan nace, mun gode Ubangiji da jinkansa ya baka ingantacciyar lafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun sani cewa a yanzu kafi lafiya fiye da yadda kake a da. Muna ganin hakan ne da takunka, nisan tafiyar da kake ci gaba da yi kasashen ketare. Ubangiji ya karo maka maka shekaru cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

"Sai dai, Ina fatan miliyoyin 'yan kasa sun samu damar morar wani bangaren daga cikin lafiyarka ta hanyar samun cigaba wajen inganta asibitocin kasarmu.
"Abun takaici shi ne, duk da irin tarin manyan alkawuran da ka yi, zaka bar mu cikin matsanancin talaucin da yafi na baya da kazo ka same mu a ciki, wannan rashawar da muka yi zaton za a kawo karshenta ta zama ruwan dare.
"A sakona na Kirsimetin shekarar da ta gabata, na nuna yadda tayi wa dokar kasa hawan 'kawara ta hanyar ragewa wajen girmama da bin dokokin dokar tarayya. Dukkanmu shaidu ne."

- A cewar Kukah.

Har ila yau, yayi jinjina ga shugaban kasa bisa kokarin da yayi a bangaren kayan masarufi sannan yana kokarin kawo karshen magudi a bangaren zabe.

"Kana ganin zan yarda ka sani amma ba kayi komai ba game da tikitin musulmi da musulmi a jam'iyyarka? Duk da haka, muna fatan zaben mara magudi."

Kara karanta wannan

NigComSat: Buhari ya dauko wani dan jiharsu, ya ba shi babban matsayi

Kukah ya koka game da garkuwa da "yaran da har yanzu ke dajika, hannayen miyagun mutane" sannan ya bukaci 'yan Najeriya su "sa ido" sannan yayi kira ga canza matakai a al'umma don tube tsagerun shugabanni maza da mata daga karagar mulki wadanda suka shirya mayar da Najeriya filin daga.

"Wannan ita ce Kirsimeti ta karshe a mulkin shugaban kasa. Ya kamata dukkanmu mu yi aikinmu saboda muna da damar zaban sabbin shugabanni.
"Kada ku cire rai Ubangiji bai gama da mu ba. Ku zabi shugabanni wadanda, a ganinku suke kaunarku, za su kula da mu, za su yi kuka tare damu, za su yi dariya da mu. Ku dubi gaba kada ku duba baya."

- A cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel