Wani Abun Fashewa da Ake Tsammanin Bam Ne Ya Tashi a Jihar Yobe

Wani Abun Fashewa da Ake Tsammanin Bam Ne Ya Tashi a Jihar Yobe

  • Wani abu da ake tsammanin 'Bam' ne aka dasa ya fashe a jejin Nayinawa, Damaturu, babban birnin jihar Yobe
  • Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, yace mutum ɗaya ya jikkata kuma an tura dakarun kwance Bam
  • Wani ganau yace da suka je ganin abinda ya faru, sun ga Kurfi da Wuƙa a wurin da aka ji ƙara mai matuƙar ƙarfi

Yobe - Almajiri ɗan shekara Bakwai ya jikkata bayan wani abu da ake zaton Bam ne ya tashi a yankin Dajin Nayinawa, Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Channels tv ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Litinin ɗin nan lokacin da aka jiyo wata ƙara mai ƙarfi daga wurin hakan ya sa mutane suka fara gudun neman tsira.

Taswirar jihar Yobe.
Wani Abun Fashewa da Ake Tsammanin Bam Ne Ya Tashi a Jihar Yobe Hoto: channels
Asali: UGC

Babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadin lamarin a cewar rahotannin da muka samu kuma babu tabbacin abinda ya fashe a wurin zuwa yanzun.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan Arewa Ya Rantsar da Shugaban Ma'aikata Da Sabbin Ciyamomi 17 a Jiharsa

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, yace tuni hukumarsu ta tura jami'an sashin kwance Bam zuwa yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Eh tabbas mun samu labarin abinda ya faru amma dai yanzun babu wasu cikakkun bayanai. Mun tura tawagar dakarun kwance Bam zuwa wurin, zamu sanar da ku halin da ake ciki."
"An ɗauki Almajirin zuwa Asibiti domin kula da lafiyarsa saboda shi kaɗai ne ya samu rauni."

Mun gano wasu abubuwa a wurin fashewar - Ganau

Wani Ganau ya yi ikirarin cewa sun gano Kurfi da Wuka a kan tabarma a wurin da fashewar ta auku.

Mutumin mai suna Adamu Hassan yace:

"Na ɗauki lokaci mai tsawo rabon da mu ji ƙara irin wannan. Ina hanyar zuwa kasuwa lokacin da lamarin ya auku, da muka ƙarisa wurin, idona ya gane mun Kurfi, da Wuƙa da wasu kayayyaki."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Ɗalibai Biyu Na Wata Jami'a a Najeriya Sun Mutu a Ɗakin Kwana

Jihar Yobe na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso gabas da matsalar yan ta'addan Boko Haram ta shafa. Sauran jihohin sun haɗa da Adamawa da Borno.

Rahoto ya nuna cewa har yanzun babu tabbacin ko fashewar ranar Lahadi na da alaƙa da 'yan ta'addan.

Wannan na zuwa ne watanni Bakwai bayan makamanciyar wannan fashewar ta faru a gundumar Abasha, ƙaramar hukumar Gashuwa, jihar Yobe.

A wani labarin kuma wani mummunan hatsarin Mota ya laƙume rayukan mutane 14 tare da jikkata wasu a jihar Kano

Hukumar kiyaye haɗurra ta tabbatar da ƙonewar Fasinjoji 14 har Lahira nan take, yayin da wata mata ta ce ga garinku nan a Asibitin Malam Aminu Kano.

Bayanai sun ce Hatsarin ya faru ne yayin da wata Motar Bus ta Kano Line ta yo taho mu gama da wata Jeep a kan babban Titin Gaya-Wudil.

Asali: Legit.ng

Online view pixel