Bidiyon Kyakyawar Baturiya da Gudu Tana bin Matashi Bakar Fata don ta Karba Lambarsa

Bidiyon Kyakyawar Baturiya da Gudu Tana bin Matashi Bakar Fata don ta Karba Lambarsa

  • Wata kyakyawar baturiya ta bayyana a bidiyo tana bin kyakyawan matashi bakar fata domin ta samu ta karba lambar wayarsa
  • Amma kafin ta dinga bin shi, matashin ne ya fara durkusawa ya bai wa budurwa balan-balan tare da sumbatar hannunta
  • Zai yuwu ganin hakan ne yasa budurwar ke son mayar masa da alheri da soyayyar da ya nuna mata inda ta bi shi har ta karba lambarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani matashi bakar fata ya hadu da wata kyakyawar budurwa baturiya kuma ya yanke hukuncin taya ta a karon farko cike da dabara da kwarewa a soyayya.

Ya tunkari budurwar ta bayanta inda ya taba ta a kafada tare da bata kyautar kyakyawar balan-balan.

Oyinbo Lady
Bidiyon Kyakyawar Baturiya da Gudu Tana bin Matashi Bakar Fata don ta Karba Lambarsa. Hoto daga @mufasatundeednut
Asali: Instagram

Kyakyawar budurwar ta karba ba tare da bata lokaci ba, amma ba a hakan aka tsaya ba. Matashin ya durkusa da guiwarsa a kasa tare da sumbatar hannunta yayin da ta mika masa babu jinkiri a cikin jama'a.

Kara karanta wannan

Kada Ki Takura ni: Matashi Yayi Watsi da Budurwar da ta ki Shi Makaranta, Yanzu take bibiyarsa

Amma ana kammala wannan abu mai kama da soyayya, matashin ya tashi tsaye inda ya cigaba da tafiyarsa ba tare da ya sake waiwayenta ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Budurwar ta bi shi

Ta yuwu wannan kyautatawa da matashin yayi wa baturiyar ya narkar mata da zuciya, hakan yasa ta ranta da gudu har ta iske shi.

Daga nan ta karba lambar wayarsa, ta yuwu kiransa zata yi daga bisani.

Jama'a sun yi martani

Tuni wadanda suka kalla bidiyon suka garzaya sashin tsokaci inda suka dinga tofa albarkacin bakunansu kan abinda ya faru a bidiyon da @mufasatundeednut ya wallafa a shafinsa na Instagram.

@obaksolo tace:

"Tabdijan, budurwa idan kika gwada wannan a Najeriya, sauran ke ya ragewa."

@ogbolor yayi tsokaci da:

"Kun dai ga yadda ta dinga gudu tana bin shi ko... A nan maza shan mari suke yi idan guiwarsu ta taba kasa a cikin jama'a."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

@_surprisesbyrose tace:

"Darasi a nan shine, ka nuna kauna a duk inda ka ga dace daidai iyawarka."

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa kyakyawa a TikTok wacce ke aiki matsayin 'yar aiki a Dubai tayi bidiyo inda take yi wa masu mata dariya martani.

Tace mutane suna mamakin dalilin da yasa take 'yar aikin gida a Dubai duk da zata iya samun kudi da irin diri da surar da take da shi.

A martanin jama'a kan ra'ayinta akan aikin da take yi, budurwar ta bayyana cewa bata damu ba kuma ta mayar da hankali kan abinda ya kai ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel