Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani

  • Wata kyakyawar budurwa ta yi watsi da girman kai inda ta fice zuwa Dubai domin zama 'yar aikin gida wanda hakan yasa ake zundenta
  • A daya daga cikin bidiyoyinta na TikTok da tayi a Dubai, budurwar ta bayyana cewa, bata damuwa da sukarta da jama'a ke ta yi ba
  • Daga cikin wadanda suka yi martani kan bidiyon da ta wallafa a TikTok, akwai wacce tace ba za ta damu idan ita ma zata zama 'yar aiki a kasar waje

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata matashiyar budurwa kyakyawa a TikTok wacce ke aiki matsayin 'yar aiki a Dubai tayi bidiyo inda take yi wa masu mata dariya martani.

Tace mutane suna mamakin dalilin da yasa take 'yar aikin gida a Dubai duk da zata iya samun kudi da irin diri da surar da take da shi.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Zukekiyar Baturiya Ta Garzayo Najeriya Wurin Saurayi Wurin Matashi

House Maid
Bidiyo: Kyakyawar Budurwa ta Koma Aikin Boyi-boyi a Dubai, Tayi wa Masu Zundenta Martani. Hoto daga TikTok/@yallmeetmina
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tana da buri

A martanin jama'a kan ra'ayinta akan aikin da take yi, budurwar ta bayyana cewa bata damu ba kuma ta mayar da hankali kan abinda ya kai ta.

Jama'a da yawa a sashin tsokacin budurwar dake aiki a kasar ketare sun bayyana irin abinda suke fuskanta yayin da suke aikin gida a kasashen waje.

Ga bidiyonta:

A yayin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya samu tsokaci masu yawa da dubban jinjina.

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin tsokacin. Ga su kamar haka:

this-be his Bae tace:

"Gara ki zama mai aikin gida da ki zama mai bayar da jikinta... Kudi ba zai saka ni wannan rashin hankalin ba."

Mhiz Gloria Sunday tace:

"Sak abinda wani ya fada min yau. Dube ki kyakyawa da ke kike aikin gida, na tausaya miki."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yaro Ya Tsokani Mahaifiyarsa Mai Juna Biyu, Ta Daura Masa Kwallon Kankana Don Ya Ji Yadda Abun Yake

damah 93 tace:

"A'a 'yar uwa, nima ina gwagwarmayar aiki a nan."

Mummoraa yace:

"Ko akwai wata hanya da zan tafi Dubai din nima?"

Silver_best3 tace:

"Ke, ai wannan ne madogara sosai. Idan kin ga wata damar ki sanar min."

Moray Mohammed tace:

"Ina bukatar aiki, ina matukar bukatar taimako. A Tanzania nake da zama."

Smallie tace:

"Ina da ra'ayin aikin da kike yi... Ya kika same shi."

Nagode wa Najeriya da ta Bani Ilimi Nagartacce, Mai Arha: Matashin Najeriya Dake Digirin Digirgir a Amurka

A wani labari na daban, wani dalibin Najeriya dake karatun digirinsa na uku a Amurka ya mika sakon godiyarsa gida Najeriya kan gatan da ya samu a fannin ilimi.

Kamar yadda matashin mai suna Ebuka Peter Ezeugwu ya bayyana, da ilimi mai arha kuma nagartacce na Najeriya da ya samu ne yasa har ya iya zuwa kasar waje.

Ebuka a halin yanzu yana karatun digirinsa na uku a fannin injiniyanci a jami'ar Minnesota.

Kara karanta wannan

Bidiyon Nasiha Mai Ratsa Zuciya da Magidanci Yayi wa Matashi Bayan Ya Ganshi Yana Tadin Mota da Budurwa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel