Kada Ki Takura ni: Matashi Yayi Watsi da Budurwar da ta ki Shi Makaranta, Yanzu take bibiyarsa

Kada Ki Takura ni: Matashi Yayi Watsi da Budurwar da ta ki Shi Makaranta, Yanzu take bibiyarsa

  • Wata tattaunawa da aka yi a WhatsApp tsakanin saurayin da tsohuwar budurwarsa wacce ta ki shi shekarun da suka gabata ya tada kura
  • A tattaunawar, budurwar ta sake nemo matashin wanda yanzu yake kasar waje, ya ginawa mahaifiyarsa gida kuma yana gina nashi.
  • Cike da abun mamaki take rokonsa da ya aureta amma sai ta sha mamakin tsabar wulakancin da yayi mata har ta kai ga ya toshe lambarta

Wani matashi ya caccaki wata budurwa wacce ta ki shi shekarun da suka gabata lokacin da suke makaranta amma daga jin yayi kudi kuma yana kasar waje ta zo tana so ya aureta.

Kamar yadda tattaunawa tsakanin budurwar mai suna Sharon Eze da matashin mai suna Obi a WhatsApp wanda @jon_d_doe ya wallafa a Twitter ta nuna, an so jin ta bakin mutane ko budurwar ta cancanci a tausaya mata.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sauyawar Wata Zukekiyar Budurwa Ya Haddasa Cece-Kuce A Yanar Gizo, Ta Kara Kyau Da Haduwa

Matashi
Kada Ki Takura ni: Matashi Yayi Watsi da Budurwar da ta ki Shi Makaranta, Yanzu take bibiyarsa. Hoto daga @don_d_doe
Asali: Getty Images

A yayin da ta fara yi wa Obi magana, budurwar ta gabatar da kanta sannan ta sanar da shi daga inda ta samo lambar shi.

Sharon tana son ya aureta

Sharon da alamu ta gano irin cigaban da matashin ya samu bayan da ta ki shi a baya. Ta dinga yabawa matashin mazaunin kasar wajen kan ayyukan da yake yi da kuma wanda yayi wa mahaifiyarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A lokacin da Obi ya tambayeta ya batun iyali, ta gaggauta sanar masa cewa bata da aure inda take rokonsa da ya zo ya kwasheta.

Obi ya caccaketa kan yadda ta bukaci ya aureta. Ya tunatar da Sharon yadda ta ki shi a baya saboda a cewarta shi ba ajinta bane kuma tana da manyan mutane da ke kashe mata kudi.

Daga bisani Obi ya toshe lambarta bayan ya zazzaga mata fada kan cewa ta kiyaye shi kuma kada ta sake damunsa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

Ga wallafar:

Jama'a sun yi martani

@Mrodanz yace:

"Kamar yadda hannun agogo yake tafiya. Bayan wadannan 'yan mata sun gama sheke ayarsu da mazan aure, sai su zo suna son auren sa'o'insu wadanda suke gani a talakawa shekarun baya."

@groovepapi yace:

"Wadannan ne matsalolin. Mata suna tunanin zasu sheke ayarsu a shekarunsu na 20 kuma su yi aure da mazan kwarai daga baya. A gaskiya ba haka abun yake ba.
"Daga baya a rayuwa ne suke ganewa idan sun yi kwantai basu samun maza kamar baya."

@mrbluprint yace:

"Mata suna son rayuwar jin dadin kuma duk wanda zai iya samar musu da abun bukata, sai su neme shi.
"Zata komawa tsohon saurayinta saboda tayi sanyi. A gare ta, komai kawai kudi ne gaba.
"Amma ai kana da kudi yanzu, kamar yadda tace. Amma fa gayen nan yayi daidai da yayi watsi da ita."

Soyayyar Gaskiya: Bidiyon Auren Kyakyawar Doguwar Amarya da Wadan Angonta ya Janyo Cece-kuce

Kara karanta wannan

Ina Ganin Wayarsa, Son shi ya Fice Daga Raina: Budurwa Ta Bayyana Dalilin Tsanar Masoyinta

A wani labari na daban, bidiyon wata doguwar amarya tare da guntun angonta ya janyo cece-kuce mai yawa a kafafen sada zumuntar zamani.

Bidiyon ya nuna lokacin da angon gajere ya shiga wurin liyafar tare da amaryarsa, wacce ko kusa ba tsawonsu daya ba.

A gajeren bidiyon da aka gani a Instagram, an ga angon yana ta tikar rawa shi kadai a wurin liyafar yayin da matarsa take zaune kuma tana magana da wani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel