Gwamnatin Buhari ta roki Saudiyya ta cire wa 'yan Najeriya takunkumin Korona

Gwamnatin Buhari ta roki Saudiyya ta cire wa 'yan Najeriya takunkumin Korona

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana bukatar ta ga kasar Saudiyya, inda ta bukaci gwamnatin Saudiyya ta cire takunkumin ga Najeriya
  • Wannan na zuwa ne yayin da kasashe da dama suka cire Najeriya a jerin kasashen da ta haramtawa shiga cikinsu
  • A baya Saudiyya ta sanya Najeriya cikin jerin kasashen ne bayan bullar sabuwar nau'in Korona ta Omicron

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bukaci kasar Saudiyya da ta dage takunkumin da ta sanya wa matafiya ‘yan Najeriya biyo bayan bullar nau'in Korona ta Omicron a kasar Afirka ta Kudu da aka gano a tsakanin wasu matafiya da aka ce sun ziyarci Najeriya.

Ambasada Zubairu Dada, Karamin Ministan Harkokin Waje ne ya yi wannan roko a ranar Asabar lokacin da ya gana da Jakadan Saudiyya a Najeriya Ambasada Faisal bin Ebraheem Al-Ghamdi, Channels Tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Korona: Alakar Najeriya da Saudiyya
Gwamnatin Buhari ta roki Saudiyya ta cire wa 'yan Najeriya takunkumin Korona | HotoL aljazeera.com
Asali: UGC

Dada a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ibrahim Aliyu ya fitar, ya bukaci mahukuntan Saudiyya da su sake duba takunkumin hana zirga-zirgar da suka sanya wa ‘yan Najeriya dangane da bullar Omicron.

Ya bukaci Saudiyya da ta yi koyi da kasashe da dama da suka saka wa Najeriya takunkumi tun da farko sannan suka dage bayan dogon nazari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya yaba da kyakkyawar alakar da ta shafe shekaru da dama tana ci gaba da wanzuwa a tsakanin kasashen biyu, Ministan ya bayyana fatansa na mayar da martani kan bukatar Najeriya a kan lokaci daga Saudiyya.

Hakan na faruwa ne yayin da ya yi alkawarin ci gaba da baiwa jakadan goyon baya da hadin kai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

A nasa jawabin, Ambasada Al-Ghamdi ya bayyana jin dadinsa da kokarin da gwamnati ke yi na dakile yaduwar nau'in Omicron na Korona tare da yin alkawarin isar da sakon Najeriya ga hukumomin da abin ya shafa a gida Saudiyya.

Kara karanta wannan

Korona: Saudiyya ta yi ƙarin haske game da batun ɗage Umrah a bana

A cewar jami'in, Saudiyya ma tana da irin wadannan hukumomin da ke da alhakin sanya ido da kuma ba da shawarwari kan al'amuran da suka shafi corona.

Hakazalika ya yaba wa Ministan bisa jajircewarsa na kyautata alaka tsakanin kasashen biyu da kasar Saudiyya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Saudiyya ta sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya na wucin gadi ne a watan Disamba yayin da nau'in Korona na Omicron ya bulla a Najeriya.

Dole ne duk mai son ganawa da Buhari ya yi gwajin Korona saboda dalilai

A wani labarin, za a bukaci masu ziyara a fadar shugaban kasa da ke Abuja, su yi gwajin Korona kafin a ba su izinin shiga fadar mulkin kasar, wacce aka fi sani da Aso Rock, ko dai don ziyartar shugaban kasa ko kuma wani jami'i.

Wadanda abin ya shafa sune muhimman mutane ciki har da gwamnoni.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya ce akwai alheri da yawa a yarjejeniyar Twitter da Najeriya

Sabuwar dokar a cewar babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, za ta bukaci duk wani bako da ya yi gwajin kyauta a kofar shiga Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel