Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya

Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya

  • A karon farko, za a bude bikin bajekolin nuna fina-finai a fadin kasar Saudi Arabia bayan dage haramcin da shekaru hudu
  • A wannan bikin, za a nuna fina-finai guda 138 na duniya kuma za a karrama mace ta farko darakta a kasar, Haifa al-Mansour
  • Kamar yadda suka sanar, makasudin yin wannan bikin shi ne karfafawa da bunkasa fannin nuna fina-finai a sinima a fadin kasar

Saudi Arabia - Za a bude bikin bajekolin nuna fina-finai a karon farko a kasa mai tsarki ta Saudi Arabia a birnin Jeddah.

Wannan lamari ya na zuwa ne kasa da shekaru hudu bayan dage haramcin nuna fina-finai a kasar Saudiyya, BBC Hausa ta ruwaito.

Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya
Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Annobar da ta fi Koronar farko na tunkaro duniya, kowa ya shirya inji masana

A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya
A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

Wannan bikin fina-finai da za a gudanar a kasar zai dauki tsawon kwanaki goma. Za a nuna fina-finai 138 daban-daban daga sassan duniya.

Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya
Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

A bikin nuna fina-finan, za a karrama Haifa al-Mansour wacce ita ce daraktar fina-finai ta farko a kasar Saudiyya.

Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya
Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

Haifa al-Mansour ce ta fara fim din Wadjda inda ta lashe kyauta, BBC Hausa ta ruwaito.

Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya
Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

Kamar yadda aka gano, manufar wannan bikin bajekolin nuna fina-finan na kasar Saudiyya shi ne bunkasa masana'antar.

Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya
Hotuna cikin labari: A karon farko, ana bikin nuna fina-finai na duniya a kasar Saudiyya. Hoto daga BBC Hausa
Asali: Facebook

Bunkasar da ake nufi kuwa ta fuskar shiryawa da kuma kasuwanci tare da nuna fina-finan a sinima da aka bude a shekarar 2018.

Ganduje ya nada Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi 2

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada Sheikh Alaramma Malam Ahmad Sulaiman Ibrahim kwamishinan ilimi na biyu a jihar.

Kara karanta wannan

Abokan aiki na dariya suka rika min: Matar da ta ajiye aikin ɗan sanda ta rungumi noma

Kamar yadda Alaramman ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya mika godiya ga Allah madaukakin Sarki tare da mika godiya a madadinsa da iyalansa ga Gwamnan.

Kamar yadda wallafar tace:

"Godiya ta tabbata ga Allah. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki. Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammadu S. A. W.
"Bayan haka, a madadina da na iyalaina da al'ummar da ta ke tare da mu, muna mika godiya mai tarin yawa ga mai girma Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduja, Khadimul Islam, bisa nada ni da yayi a kwamishina na 2 a hukumar ilimi ta jihar Kano.
"Ina rokon Allah ta'ala ya sanya alheri, yasa mana albarka cikin wannan kujera da ya ba mu dan ya jarabce mu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel