Saurayi ya biya kudin abincinsa shi kadai bayan budurwa ta je mishi da kawaye 2

Saurayi ya biya kudin abincinsa shi kadai bayan budurwa ta je mishi da kawaye 2

- Wata budurwa 'yar Najeriya ta bayar da labarin yadda saurayinta ya tozarta ta a gaban kawayenta

- Ta ce kafa-da-kafa ta gayyaci kawayenta don su je su kwashi gara a wurin cin abinci da zaton saurayinta zai siya musu

- Sai da suka kammala cin abincin ya murje idanunsa ya lallaba ya biya kudin nasa su kuma ya bar su a wurin

Cikin takaici da alhini wata budurwa mai amfani da suna Reddishwine3 a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta bayyana yadda saurayinta ya tozartata a gaban kawayenta.

Ta ce sun yi za su fita cin abinci ita da saurayinta, sai ta gayyaci kawayenta suka tafi tare. Sai da suka kammala cin abincin tas, ya mike tsaf ya tafi ya biya kudin nashi abincin ya bar su a nan.

Ta yi wallafar ne ranar Juma'a, 8 ga watan Janairu, inda tace lallai wasu mazan ba su da tausayi balle imani.

Ta ce wannan dabi'ar ta tabbatar da cewa saurayin bai san abinda ya dace ba. Ya kamata ya duba cewa tare da kawayenta take ya rufa mata asiri ya biya kudin.

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Maiduguri bayan an babbaka sojan da ya harbi farar hula 4

Saurayi ya biya kudin abincinsa shi kadai bayan budurwa ta je mishi da kawaye 2
Saurayi ya biya kudin abincinsa shi kadai bayan budurwa ta je mishi da kawaye 2. Hoto daga @Reddishwine3
Source: Twitter

Wannan wallafar ta janyo cece-kuce iri-iri a kafar sada zumunta, inda wasu suke ganin yayi daidai kuma sun ga laifinta, don ya kamata ta sanar masa cewa za ta je da kawayenta don ya shirya.

Wasu sun bayyana ra'ayoyinsu, inda suke cewa ya kamata ya biya saboda gudun tozarta ta a gaban kawayenta.

KU KARANTA: Bidiyon yaro yana kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba ya nishadantar

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata matar aure mai shekaru 20 mai suna Suwaiba Shuaibu a kan zarginta da sokawa wata Aisha Kabir wuka ana sauran kwanaki kadan aurenta.

An gano cewa Aisha ce wacce Malam Shahrehu Alhaji Ali, mijin wacce ake zargin zai aura a ranar 9 ga watan Janairu a kauyen Gimawa, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce an nema amaryar an rasa amma daga baya sai aka ga gawarta a wani kango.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel