Jigo a kudu ya gano hanyar lallabar 'yan Arewa su mika mulki kudu a 2023

Jigo a kudu ya gano hanyar lallabar 'yan Arewa su mika mulki kudu a 2023

  • Wani babban malamin addinin kirista ya bayyana cewa, dole ne a roki 'yan Arewa idan ana son kai shugabancin Najeriya kudu
  • A cewarsa, ba abu ne mai sauki ba a dauki mulki a kai kudu ba tare da amincewar 'yan Arewa ba
  • Ya kuma bayyana abin da ya fahimta da mulkin shugaba Buhari da ake ci a halin yanzu, wanda ake kokawa

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, Tunde Bakare, mai kula da cocin Citadel Global Community, ya ce duk wanda ke son jagorantar Najeriya dole ne ya tattauna da yankin Arewacin kasar.

Da yake magana a wata hira da ThisDay, Bakare ya ce yana shakkar idan Arewa za ta bar mulki cikin dadin rai.

Ya ce babu wani sashe na kasar "da zai iya cin zabe da kansa" saboda haka hadin gwiwa ne ya dace da nasarar zabe.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan fashi suka harbi mai shagon POS saboda kin basu kudi cikin dadin rai

Duk dan kudu da ke son shugabancin Najeriya dole ne lallabi 'yan Arewa, ini jigo a kudu
Tunde Bakare | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa, a halin da ake ciki babu wani abu da ya rage na arziki a yankin Arewacin Najeriya sai ikon mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa, cewa yayi:

“A gaskiya zan ce, kusan duk abubuwan da ke a arewa a zamanin Ahmadu Bello babu su yanzu. Masana'antun masaku inda suka mamaye yanzu babu su. Tarin gyada, da sauransu, kawai abin da suke da shi shine abin da suke rikewa. Suna da mulki.
“An tsara Najeriya ta yadda babu wani sashe da zai iya cin zabe da kansa. Dan kudu ba zai iya cin zabe ba ba tare da ya kai Arewa ba, sannan dan Arewa ba zai iya cin zabe ba ba tare da ya kai kudu ba.”

Dangane da kimanta nasarorin da gwamnati mai ci ta samu a cikin shekaru shidan da suka gabata, Bakare ya ce abubuwa da yawa sun tabarbare duk da cewa gwamnati sun yi iya "kokarin su".

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

A cewar Bakare:

“Abubuwan da muke tsammanin sun yi yawa. Wani lokaci, nakan zauna ina tunanin cewa, ah, a matsayina na shugaban kasa, shin Buhari bai ragargaza kansa ba kuwa, saboda tsammanin 'yan Najeriya ya yi yawa lokacin da ya hau mulki."

Ya bayyana yadda rashin lafiya ya lalata wa'adin shugaba Buhari na farko tare da cewa, shugaban bai taba zaton irin haka ba.

Shugabanci a 2023: Shugaban APC Buni da tawagarsa sun ziyarci Tinubu a gidansa

Alamu sun nuna burin zama shugaban kasa na jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya samu babban ci gaba a ranar Lahadi, 24 ga watan Oktoba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan karin darajar cewa bai rasa nasaba da ziyarar shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC mai mulki kuma gwamnan jihar Yobe ba, Mai Mala Buni, da tawagarsa ga tsohon gwamnan na Legas.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Tawagar Buni, don haka, ta shiga cikin manyan shugabannin APC da suka ziyarci Tinubu a London da Legas a cikin watanni uku da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel