Aisha Khalid
4688 articles published since 22 Agu 2019
4688 articles published since 22 Agu 2019
Kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i ta caccaki gwamnatin tarayya kan yadda ta biya albashin kwana 18. ASUU tace su malamai ne ba ma’aikatan wucin-gadi ba.
Gwamna Ganduje na Kano ya shiga tsakanin shugaban masu rinjayen majalisar wakilai,Alhassan Doguwa da Murtala Sule Garo sakamakon Rikicin da ya barke tsakaninsu.
Kotun Majistire ta umarci a sambadawa 'yan TikTok biyu, Nazifi da Unique pikin Bulalu 20 kowanensu bayan kama su da laifin zagin gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje
An habe mutum daya sakamakon farmakin da aka kai wa magoya bayan ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a Eberi dake Omuma a Ribas.
Mambobin majalisar zartarwa ta kungiyar malaman jami’o’i masu koyarwa, ASUU,ta shiga ganawar gaggawa Saboda biyan albashin rabin wata da gwamnatin tarayya tayi.
Tsohon ‘dan majalisa da ya wakilci mazabar Kudan a majalisar jihar Kaduna tsakanin 2011 zuwa 2019, Alhaji Danlami Dan Inna Likoro, ya kwanta dama ranar Lahadi.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta damke wasu ‘yan kasuwar Fakistan a filin jiragen sama na Murtala Muhammad a Legas da 8kg na hodar iblis.
Manyan ‘yan majalisar Shura na kungiyar ISWAP,Ali Kwaya da Bukar Mainoka tare da wasu ‘yan ta’addan sun mutu sakamakon bama-bamai da sojin sama suka Harba musu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta dakile wani mummunan farmaki da wasu da ake zargin mambobin ISWAP ne suka kai caji ofis a birnin Magumeri dake jihar Borno.
Aisha Khalid
Samu kari