An Bindige Mutum 1, Wasu Sun Jigata Yayin da ‘Yan Daba Suka Kai Hari Kan Magoya Bayan Atiku

An Bindige Mutum 1, Wasu Sun Jigata Yayin da ‘Yan Daba Suka Kai Hari Kan Magoya Bayan Atiku

  • Yan daba sama da 30 dauke da adduna da bindigogi sun kai hari kan tawagar kamfen din Atiku Abubakar a garin Omuma na jihar Ribas
  • Kamar yadda shugaban tawagar na Omuma, Nnamdi Nwogu ya bayyana, an harbe daya daga cikin hadimansa yayin da suke manna fostoci a wani yanki
  • Bayan sun kwashi Udochukwu da aka datsa da adda, an tabbatar musu cewa maharan zasu biyo su kuma shugabannin siyasa ne suka sa su

Ribas - An habe mutum daya sakamakon farmakin da aka kai wa magoya bayan ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a Eberi dake karamar hukumar Omuma ta jihar Ribas.

Kamfen din Atiku Abubakar
An Bindige Mutum 1, Wasu Sun Jigata Yayin da ‘Yan Daba Suka Kai Hari Kan Magoya Bayan Atiku. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wadanda lamarin ya ritsa da su shine shugaban kwamitin kamfen din Atiku na kasa a Omuma, Nnamdi Nwogu.

Kara karanta wannan

Manoma sun huta, sojoji sun sheke wani kasurgumin shugaban 'yan bindiga a Zamfara

Nwogu wanda ya tabbatar da farmakin ranar Litinin, yace sama da matasa 30 dauke da adduna da bindigogi suka far masa, hadiminsa da wasu mutum uku yayin da suke manna fostocin ubangidansu a Eberi dake Omuma a ranar Lahadi.

Ya zargi cewa shugabannin siyasan yankin ne suka bada umarnin kai musu farmakin inda yace hadiminsa mai suna Udochukwu an yankesa kuma an harbesa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Nwogu yace Udochukwu yana cikin matsanancin hali a wani asibiti da ya boye sunansa a Fatakwal.

Kamar yada yace:

“Kwanaki uku da suka gabata na bai wa yarana fostocin Atiku Abubakar su manna a karamar hukumata.
“Kuma jiya na kira daya daga cikinsu Udochukwu da wani abokina da su zo su taya ni sanyawa.
“Bayan mun isa wurin, na ga fostocin a wasu wurare. Amma na gane cewa ba a sanya su a tsare ba a wani wuri da ake kira Eberi Omuma.

Kara karanta wannan

2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi

“Nace toh tunda gani ai sai in gyara. Muna cikin sanyawa ne muka ji matasa sama da 30 dauke da adduna da bindigogi sun biyo mu. Sun yanki Udochukwu tare da fatattakata da abokina.
“Koda nayi kokarin ceton yarona da suka sara yana zubar da jini, sun sake biyo mu tare da harbinsa.
“Da kyar muka kwashe shi zuwa asibiti. Bayan an saka masa ruwa, an sanar damu cewa suna biye da mu.”

Kakakin tawagar kamfen din Atiku a Ribas, Dakta Leloonu Nwibubasa ya kushe faruwar lamarin kuma yayi kira ga ‘yan sanda da su tsunduma bincike da wuri.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-koko, tace a jirace ta.

Yan Daba Ɗauke da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku a Kaduna

A wani labari na daban, Rahoton da muke samu ya nuna cewa wasu yan Daba sun farmaki magoya bayan PDP a Ranches Bees Stadium, Kaduna, wurin gangamin taron ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rubutu da ya saki a shafinsa na dandalin Facebook ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel