Kotu Tayi Umarnin a Yi wa ‘Yan TikTok Bulala 20 Kan Zagin Ganduje

Kotu Tayi Umarnin a Yi wa ‘Yan TikTok Bulala 20 Kan Zagin Ganduje

  • Kotu ta yankewa Uniquepikin da Nazifi Muhammad hukuncin bulala ashirin-ashirin kowannensu sakamakon batawa Gwamna Ganduje suna da suka yi
  • Alkali Aminu Gabari na kotun majistare din bayan kammala sauraron shari’ar, ya kara da umarni ga matasan da su share farfajiyar kotun tsawon kwana 30
  • A wani bidiyo da masu wasan barkwancine suka saki a TikTok, sun ayyana Ganduje matsayin ‘dan siyasa mai cin rashawa wanda ke siyar da duk filin jihar da ya ci karo da shi

Kano - Wata kotun majistare dake zama a jihar Kano tayi umarnin ba wa Uniquepikin da Nazifi Muhammad, bulala ashirin kan batawa Gwamna Abdullahi Ganduje suna a wani bidiyon TikTok.

Masu bidiyon barkwancin an kama su cikin kwanakin nan tare da gurfanar dasu a gaban kot bayan wani bidiyonsu ya yadu suna alakanta Ganduje da rashawa.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Zagin Ganduje a TikTok
Kotu Tayi Umarnin a Yi wa ‘Yan TikTok Bulala 20 Kan Zagin Ganduje Hoto: qed.ng
Asali: UGC

An kai su gaban alkali kan laifuka biyu da ake zarginsu da shi.

A yayin zaman kotun, Alkali Aminu Gabari yayi umarnin yi wa kowanne daga cikinsu bulala 20 sannan su share farfajiyar kotu na tsawon kwanaki 30z

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta umarci kowanne daga cikin masu wasannin barkwancin da ya biya N10,000.

A bidiyon, masu wasan barkwancin sun ayyana Ganduje da ‘Dan siyasa mai cin rashawa wanda ke siyar da kowanne fili da ya ci karo da shi na jihar.

“Wannan babi ne dake bayani kan Ganduje. Kuma wanene Gandujen nan? Shi ne mijin shahararriyar mata kuma uban Balarabe. Asalinsa ‘Dan jihar Kano ne. Halayen Ganduje sune kamar Haka: Gwamna ne dake son barci.”

- Suka ce.

“Amma ya zama abun zargi a idanun jama’ar Kano. Idan za a bayyana kadan daga cikin halayensa da baiwoyinsa, in har ya ga fili a Kano toh tabbas sai ya kwashi rabonsa. Domin karin bayani kan hakan, ko dai ya siya ko kuma ya killace, a karshe dai wani abun tambaya sai ya taso.”

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

A wani labarin kuma kun ji cewa Alkali ya umarci a tsare taurarin masu amfani da shafin TikTok biyu a gidan gayaran hali

Wasu taurari a shafin Tik-Tok, Mubarak Muhammad da Nazifi Muhammad sun ɗebo ruwan dafa kansu bayan sun yi bidiyon da ake zargin ya taba mutuncin mai girma gwamnan Kano.

Dakarun yan sanda sun damƙesu tare da makasu gaban Kotun majirtire, kuma basu wahal da Kotu ba sun amsa laifukansu bayan karantosu a zaman. Alkali ya nemi a ci gab ada tsaresu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel