An kama wani mutum yana kwanciya da 'yarsa ta cikinsa

An kama wani mutum yana kwanciya da 'yarsa ta cikinsa

An kama wani mutum mai suna Uchena Elumadu, inda aka bayyana cewar yana kwanciya da 'yarsa ta cikin sa mai shekaru 15 da haihuwa a duniya, sannan kuma yasha bata magani dan gudun kada ta dauki ciki.

News Agency of Nigeria (NAN) sun rawaito cewar, an kama mutumin ne ranar Lahadi 24 ga watan Satumba, inda mai magana da yawun 'yan sandan jahar Legas mai suna, SP Dolapo Badmos ya tabbatar da hakan.

An kama wani mutum yana kwanciya da 'yarsa ta cikinsa
FOlis

Alokacin da shashin bincike na hukumar 'yan sanda suke tuhumar sa, mutumin dai ya bayyana cewar shi yana sana'ar tireda ne. Acewar mai magana da yawun 'yan sandan, wani makwabcin mutumin ne wanda suke zaure tare a Martins Street, New Oko Oba, a Agege jahar Legas ya kawo karar wanda ake binciken, inda akace ya lalata yarinyar da take zauren karatu na JSS3.

Badmos ya kara dacewa; " yarinyar da abun ya faru da ita tace, sauda yawa mahaifin nata yasha tashinta cikin tsakiyar dare kuma ya kwanta da ita, mafi akasari hakan yafi faruwa idan mahaifiyar ta bata nan taje aikin dare, domin mahaifiyar nata tana aiki a wani waje dake hade da filin sauka da tashi na jirgin sama".

" A daren 19 ga watan satumba ne, mahaifiyar nata ta gane wanda ake zargin yana kwanciya da 'yarsa inda nan take ta tona masa asiri, koda wani makwabcin nasu yaji abunda ke faruwa, sai kawai ya garzaya wajen 'yan sanda".

Inda nan take aka kai yarinyar asitin 'yan sanda dake Ikeja Police College inda anan ne ake dubata tare da cibiyar Mirabel na LASUTH.

Haka kuma, CP Fatai Owoseni, wato kwamishinan 'yan sanda yace mutumin da ake tuhuma, za'a turashi kotu inda zai girbi abinda ya shuka. Kwamishinan ya bayyana cewar hukumar bazata taba yarda da laifufuka wa'anda suka jibanci irin wadannan na badala ba da kuma sauran laifufuka masu kama da wannan a jahar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel