Tukunya mai tsohon tarihi
- An gano wata tukunya da mafi girma da kuma yawan shekaru a jihar Kano
- Wasu masu aikin gini ne suka hako tukunyar
- Za a kai tukunyar dakin gwaje-gwaje na kimiyya don gano yawan shekarunta
Wasu mutane masu aikin gini a kauyen Rummawa Rangaza a karamar hukumar Ungoggo ta jihar Kano ne suka gano tukunyar.
Ma’aikatan na aikin haka fandishon wani gini ne a kauyen, yayin da suka ci karo da tukunyar a ranar Laraba 21 ga watan Satumba.
Shugaban Kula da gidan adana kayan tarihi na kasa da ke Gidan Makama a Kano, Mustafa Mohammed Bataka ya yi karin haske game da tukunyar a hirarsa da ‘yan jaridu, yana mai cewa, tukunyar tafi kowacce tukunya da ke hannunsu girma, a gidan adana kayayyakin tarihi, sannan ya kuma ce, da alama tukunyar ta dade, amma ba zai iya kimanta shekarunta ba.
KU KARANTA KUMA: Sabuwa: An gano wata tsohuwar tukunya a jihar Kano
Shugaban wanda ya ziyarci wurin don ganewa idonsa, ya ce, za su zo da kwarraru wadanda za su haketa, a kuma kai ta dakin gwaje-gwaje na kimiyya a inda za a iya sanin hakikanin shekarunta a duniya.
Ana kyautata zaton cewa manyan tukwane irin wannan mutanen da, na amfani da su ne ko wajen adana ruwa, ko domin tsaro a inda ake jike-jiken magunguna, da siddabaru na tsaron gari.
Mutane da yawa ne ke ta tururuwa zuwa kauyen don ganewa idonsu, an dai taba samun irin wannan tukunya a garin Ririwai da ke karamar hukumar a Doguwa a shekarun 1980, an kuma taba samun kwatankwacinta a unguwar Nomans Land a shekarun 1990 a unguwar Sabongari duk a jihar Kano.
Asali: Legit.ng