Yan sanda sun damke wani mahaifi da ya batar da ɗiyarsa da ya haifa a Adamawa

Yan sanda sun damke wani mahaifi da ya batar da ɗiyarsa da ya haifa a Adamawa

  • Wani mutumi da aka ɓoye sunansa ya shiga hannun jami'an yan sanda bisa zargin ɓatan ɗiyarsa ta cikinsa a Adamawa
  • Mutumin yace ba shi da hannu a zargin da ake masa, domin shima neman yarinyar yake tun bayan da suka je kasuwa tare yin siyayya
  • Jami'an yan sanda sun gano wata gawar mace da ake zargin ta ɗiyar wanda ake zargi ne a garin Mayo-Belwa

Adamawa - Jami'an yan sanda a jihar Adamawa sun yi ram da wani mutumi a garin Mayo-Belwa ƙaramar hukumar Belwa, bayan sun gano wata gawa da ake zargin ta ɗiyarsa ce.

Punch ta rahoto cewa mutumin ya yi ikirarin cewa ɗiyar tasa ta ɓata ne a hanyarsu ta komawa gida bayan sun je siyayya a kasuwa.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, shine ya tabbatar da cafke mutumin ranar Alhamis.

Jihar Adamawa
Yan sanda sun damke wani mahaifi da ya batar da ɗiyarsa da ya haifa a Adamawa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin yan sandan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wanda ake zargin yana hannun yan sanda, ana cigaba da bincike kan lamarin. Ana zargin mutumin da hannu a ɓatan ɗiyarsa yar shekara 16."
"Ya faɗa mana cewa ya baiwa yarinya kayayyakin abincin da suka siya a kasuwa, ya umarce ta takai su gida."
"A bayanin da ya mana, bayan ya dawo gida ne ya fahimce cewa ɗiyar tasa bata dawo ba. Amma mun gano wata gawa da muke zargin ta yarinyar ce a garin Mayo-Belwa."

Wane hali ake ciki yanzu?

Kakakin yan sandan ya tabbatar da cewa jami'ai zasu tsananta bincike kuma duk wanda aka kama da hannu zai fuskanci doka.

Ɗaya daga cikin mazauna garin Mayo-Belwa, Malam Sahabi Joda, wanda maƙoci ne ga wanda ake zargi, yace lamarin ya faru ne ranar Talata.

Kara karanta wannan

An kuma, Miyagun yan bindiga sun kutsa fadar Basarake, sun yi awon gaba da shi a jihar Katsina

Joda ya ƙara da cewa karo na ƙarshe da suka ga wanda ake zargin da ɗiyar tasa shine kwanaki uku da suka gabata, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A wani labarin kuma wani magidanci ya nemi a katse igiyar aurensa da natarsa saboda kwata-kwata bata yin wanka

A rahoton Aminiya, matar ba ta ji daɗin wannan zance na mai gidanta ba, wanda suka kwashe shekariu biyu suna gina soyayyarsu bayan Aure.

Matar dake zaune a Uttar Pardesh na Kasar Indiya, ta yi gaggawar garzayawa zuwa wurin wata ƙungiyar dake fafutukar kare hakkin mata domin ta shiga cikin lamarin ta hana kudirin mijinta ya cika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel