Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

  • Wani magidanci a ƙasar Indiya ya nemi a raba aurensa da matarsa shekaru biyu da aure, saboda bata yin wanka kullum
  • Sai dai labarin baiwa matar ɗaɗi ba, inda ta garzaya wurin wata ƙungiyar kare mata, tana neman a ceto mata aurenta
  • Kungiyar ta yi iyakacin kokarinta wajen baiwa ma'auratan shawara domin a ganinta matsalar karama ce da zasu iya sulhunta tsakani

India - Wani mutumi ya nemi a kawo karshen aurensa da masoyiyar matarsa saboda kazama ce bata wanka kullum-kullum.

A rahoton Aminiya, matar ba ta ji daɗin wannan zance na mai gidanta ba, wanda suka kwashe shekariu biyu suna gina soyayyarsu bayan Aure.

Matar dake zaune a Uttar Pardesh na Kasar Indiya, ta yi gaggawar garzayawa zuwa wurin wata ƙungiyar dake fafutukar kare hakkin mata domin ta shiga cikin lamarin ta hana kudirin mijinta ya cika.

Read also

Yadda 'Ruwa mai tsarki' ya raba Mata da Miji da suka shekara 10 suna gina soyayya

Ma'aurata a Indiya
Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa Hoto: aminiya.dailytrust.com
Source: UGC

An shiga sasanci tsakanin ma'auratan

Kungiyar ta nemi sasanta tsakanin ma'auratan, ta hanyar kiran matar da mijinta haɗe da iyayensu domin tattaunawa da samar da mafita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin da ya shiga sasanci tsakanin ma'auratan, Bobby Bhai, ya bayyana cewa magidancin ya nuna damuwarsa kan yadda ya shafe shekaru da matar amma ta ƙi jin maganarsa wajen yin wanka.

Bhai yace:

"Mijin yace ya yi iyakar kokarinsa, amma bata ƙaunar yin wanka kowace rana, bisa wannan dalilin ne yake son a raba auren."

Shin matar ta amince ba ta wanka?

A nata ɓangaren matar ta bayyana cewa ita fa sam bata shirya katse aurenta ba da mijinta, uba ga ɗanta guda ɗaya, saboda haka tace a bashi hakuri.

Sai dai babu labari kan abinda matar tace game da ƙorafin mijinta na rashin wanka kowace rana.

Read also

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Kungiyar ta baiwa mijin shawara ya dakatar da kudirinsa na rabuwa da matarsa, domin zasu iya sasanta kansu, kuma matsalarsu ƙarama ce.

A wani labarin na daban kuma Sabbin zafafan Hotunan Jaruma Rahama Sadau a wurin daukar fim a Bollywood Indiya sun sake bayyana

Tun a baya dai Sadau ta buga hotuna a dandalinta na sada zumunta, inda tace tana aikin shirin fim da masana'antar Bollywood.

Rahama Sadau, ta saba jawo cece kuce kan shigar da bata dace da addininta ba kuma ta dora a kafar sada zumunta.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel