Allah ya yiwa Malam Musa Mai Shara da kiran Sallar Farko na Asuba a Masallacin Sultan Bello rasuwa

Allah ya yiwa Malam Musa Mai Shara da kiran Sallar Farko na Asuba a Masallacin Sultan Bello rasuwa

  • Malam Musa Mai Shara da kiran Sallar Farko na Asuba a Masallacin Sultan Bello ya rasu
  • Dattijon ya rasu ne a asibitin Barau Dikko dake jihar Kaduna
  • Sheikh Ahmad Gumi ne ya jagoranci Sallar Jana'izarsa

Kaduna - Dattijon arziki, Malam Musa Jos, wanda ya shahara a babban Masallacin Sultan Bello dake jihar Kaduna, ya rigamu gudan gaskiya.

Babban Malami, Sheikh Ahmad Gumi, ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook da safiyar Litnin, 4 ga watan Oktoba, 2021.

A cewar Malam Gumi, marigayin ya kasance mai sharan Masallacin kuma mai kiran Sallar farko ta Asuba a Masallacin.

Hakazalika shine mai fito da kayan karatu (litattafai) a duk lokacin da aka shirya karatu a Masallacin.

Malam Musa ya rasu a Asibitin Barau Dikko ne dake jihar.

Sheikh Gumui yace:

Read also

Da dumi-dumi: Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, kanin Mama Taraba, rasuwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Allah yayiwa Malam Musa Jos (Mal Musa Mai Shara mai kiran Sallar Farko na Asubah kuma Mai fito da kayan Karatu A koda yaushe na Masallacin Sultan Bello Kaduna) Rasuwa Yau a asibitin Barau Dikko

Allah ya yiwa Malam Musa Mai Shara da kiran Sallar Farko na Asuba a Masallacin Sultan Bello rasuwa
Allah ya yiwa Malam Musa Mai Shara da kiran Sallar Farko na Asuba a Masallacin Sultan Bello rasuwa Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

An yi masa Jana'iza

Gumi ya ce an yi masa Sallar Jana'iza bayan Sallar Magariba. Yayi addu'an Allah ya jikansa da rahama.

Malam Gumi da kansa ne ya jagoranci Sallar Jana'izar.

A cewarsa:

An yi masa Jana'iza bayan Idar da Sallar Magriba kamar yadda Musulunci ya tanada
Muna rokon Allah ya jikanshi ya gafarta mashi yasa Aljannah ce makomarsa da mu baki daya.

Source: Legit.ng

Online view pixel