Matsalar Tsaro: Gwarazan yan sanda sun cafke wani mai garkuwa da mutane a Kano

Matsalar Tsaro: Gwarazan yan sanda sun cafke wani mai garkuwa da mutane a Kano

  • Jami'an yan sanda sun samu nasarar damƙe wani mutumi da ake zargin ɗan garkuwa ne a ƙaramar hukumar Tsanyawa, jihar Kano
  • Mutumin mai suna, Tukur Ahmed, ya shiga hannu ne biyo bayan barazanar da ya yi wa wani cewa zai sace shi ko ƴaƴansa idan bai biya miliyan N1m ba
  • Binciken yan sanda ya tabbatar da cewa Tukur Ahmed, ɗan uwa ne ga mutumin da aka yiwa barazana

Kano - Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta cafke wani da ake zargin ɗan garkuwa da mutane ne a ƙauyen Soro Ɗaya, ƙaramar hukunar Tsanyawa, kamar yadda This day ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ranar Talata a Kano.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Yace wani mazaunin ƙauyen Danzabuwa, ƙaramar hukunar Bichi, ya shigar da ƙorafin cewa an kira shi a waya, an mishi barazanar ya biya miliyan ɗaya ko kuma a sace shi ko yayansa.

Yan sanda sun kame ɗan garkuwa a Kano
Matsalar Tsaro: Gwarazan yan sanda sun cafke wani mai garkuwa da mutane a Kano Hoto: blueprint.ng
Source: UGC

Bayan haka wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Sanarwar tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan samun wannan ƙorafi, kwamishinan yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Dikko, ya tada tawagar jami'ai bisa jagorancin SP Shehu Dahiru domin bincike da kamo waɗanda suka aikata haka."
"Nan take tawagar ta fara aiki, bayan samun wasu bayanan sirri, jami'an sun samu nasarar cafke Nasiru Ahmad, wanda ɗan asalin kauyen Soro Ɗaya ne, karamar hukumar Tsanyawa."
"Jami'an sun yi ram da mutumin ɗan kimanin shekara 28 a ƙauyen Panda, ƙaramar hukumar Keffi, jihar Nasarawa, a ranar 25 ga watan Satumba."

Me bincike ya gano?

Kakakin yan sanda yace yayin bincike, mutumin da ake zargi ya amsa laifinsa kuma ya tabbatar ta da cewa wanda ya yi wa barazana ɗin ɗan uwansa ne.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

A cewarsa, nan bada jimawa ba, hukumar yan sanda zata gurfanar da Tukur Ahmad, a gaban kotu, da zaran an kammala bincike.

A wani labarin na daban kuma Manoma Sama da 20 Sun Mutu, Yayin da Jirgin Yaki Ya Yi Kuskuren Sakin Bama-Bamai a Borno

Aƙalla mutanen ba basu ji ba basu gani ba 20 sun rasa rayukansu sanadiyyar harin jirgin yaƙi a Dabar Masara, ƙaramar hukumar Monguno, jihar Borno, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cewar wata majiya daga yankin, harin saman ya faru ne ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba da yammaci.

Source: Legit

Online view pixel