Da dumi-dumi: Allah ya yiwa Sarkin Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska, rasuwa

Da dumi-dumi: Allah ya yiwa Sarkin Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska, rasuwa

  • Bayan shekaru 48 kan mulki, Sarkin Sudan na Kontagora ya rasu
  • Gwamnan jihar Neja ya ce za'a yi rashin Sarkin matuka
  • Wannan ya biyo bayan mutuwar 'dansa da yan bindiga suka kaiwa hari a gona

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa Sarkin Sudan na masarautar Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska, ya rigamu gidan gaskiya.

Legit Hausa ta tattaro cewa Sarkin ya rasu ne da safiyar Alhamis a wani asibiti dake birnin tarayya Abuja.

Sarkin ya kwashe shekaru 47 kan mulkin Kontagora. Ya rasu yana mai shekaru 84.

Sarkin ya mutu kimanin watanni uku bayan kisan 'dansa, Yariman Kontagora.

Gwamnan jihar Neja wanda yayi sanarwar ya nuna jimanin rashin Sarkin Kontagora.

A jawabin da Sakariyar yada labaransa, Mary Noel-Berje, ta saki, yace Sarkin ya bautawa al'ummarsa cikin gaskiya da adalci kuma za'a yi kewarsa sosai.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Mutuwar masoyi abu ne mai zafi, hakazalika mutuwar mahaifi komin tsawon ransa."
"Sarkin Sudan babban alheri ne ga masarautar Kontagora, ya bautawa al'ummarsa sosai. Abinda muke bukata yanzu shine addu'ar Allah ya jikansa kuma ya yi bashi Aljanna Firdausi ",
Da dumi-dumi: Allah ya yiwa Sarkin Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska, rasuwa
Da dumi-dumi: Allah ya yiwa Sarkin Kontagora, Alhaji Saidu Umaru Namaska, rasuwa Hoto: Emergency Digest
Asali: Facebook

Yan bindiga sun bindige 'dan Sarkin Kontagora har lahira

Dan gidan Sarkin Kontagora, Alhaji Bashar Saidu Namaska, na cikin mutanen da yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari gonar Sarkin a ranar Laraba, 19 ga Mayu, 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'dan Sarkin na tare da wasu mutane ne cikin gona dake titin Zuru lokacin da yan bindiga suka kai musu farmaki.

Yan bindigan sun yi awon gaba da shanu da dama.

Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga 7 da suka kashe 'dan Sarkin Kontagora, Bashir Namaska

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Gamayyar jami'an hukumar Sojojin Najeriya da na yan sanda a karamar hukumar Kontagora sun ragargaji yan bindiga akalla guda bakwai a cikin daji a jihar Neja.

PRNigeria ta tattaro cewa kwamandan 311 Artillery, T.O Olukukun, da kwamandan yan sandan, Haruna Adamu Swapo ne suka jagoranci farkamin da aka kaiwa yan bindigan.

Jami'an tsaron sun kure musu gudu cikin daji kuma suka hallakasu. Sauran kuwa sun gudu da raunukan harbi. Daya daga cikin yan bindigan da aka kama wanda ya mutu daga baya ya gaza magana da Turanci ko Hausa, yaren Fulfulde kawai yayi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel