Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Lere, Abubakar Garba Mohammed rasuwa

Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Lere, Abubakar Garba Mohammed rasuwa

- Mutanen jihar Kaduna na alhinin rashin daya daga cikin manyan sarakunan jihar

- Iyalan basaraken sun tabbatar da rasuwar Sarkin na Lere, Abubakar Garba Muhammad

- Marigayin basaraken tsohon jami'in soja ne kuma tsohon gwamnan mulkin soja

Mai martaba Sarkin Lere, Birgediya Janar Abubakar Garba Mohammed (mai murabus) ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 77 a duniya.

Wata majiya daga garin na Lere da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa Legit.ng Hausa rasuwar sarkin.

DUBA WANNAN: Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP 11 sun dira Makurdi domin hallartar taro

Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Lere, Abubakar Garba Mohammed rasuwa
Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa Sarkin Lere, Abubakar Garba Mohammed rasuwa
Asali: Twitter

Garba ya rasu ne a safiyar ranar Asabar 10 ga watan Afrilu a Kaduna bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Marigayi Abubakar Garba ya taba gwamnan jihar Sokoto a karkashin gwamnatin mulkin soja na Badamasi Babangida.

Za a yi jana'izar marigayin a garin Lere misalin karfe 5 na yamma a cewar Premium Times.

Kazalika, wasu daga iyalan sarkin sun tabbatarwa majiyar Legit.ng rasuwar inda suka ce ya mutu bayan gajeruwar jinya.

KU KARANTA: Rundunar 'Yan Sandan Nigeria ta bawa Sarkin Bauchi lambar yabo

"Kawo na ne. Ya rasu yau Asabar da safe. Tabbas rasuwarsa babban rashi ne gare mu da dukkan iyalin," a cewar Hassan Mohammed.

Sarki Abubakar ya dare kan karagar mulkin masarautar Lere ne bayan rasuwar Umaru Sani a shekarar 2011.

Ya rasu ya bar 'ya'ya hudu da jikoki da dama.

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel