Shugaban kasa Buhari ya aika wa 'Yan Majalisa takarda, ya yi sababbin nadin mukamai a EFCC
- Shugaban kasa ya bukaci Sanatoci su tantance shugabannin majalisar EFCC
- Dr. Ahmad Lawan ya karanto takardar Muhammadu Buhari a zauren majalisa
- George Abang Ekpungu zai zama Sakataren majalisar da ke sa ido a hukumar
Abuja – A ranar Talatar nan Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabannin da za su rika sa ido a hukumar EFCC.
Jaridar Daily Trust ce ta fitar da wannan rahoto a safiyar ranar 21 ga watan Satumba, 2021.
Mista George Abang Ekpungu ya zama sakataren majalisar da za ta rika sa ido a EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.
Sauran wadanda shugaban kasar ya zaba a cikin majalisar kula da hukumar sun hada da Lukman Mohammed, Kola Adeshina da Mohammed Yahaya.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ne ya karanto wasikar Shugaban Najeriyar a lokacin da aka fara zaman majalisa a yau a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Muhammadu Buhari ya shaida wa Sanatocin kasar cewa ya nada mukaman ne kamar yadda sassa na 2 (1) da na (4) na dokar da ta kafa EFCC ta tanada.
Daily Trust tace shugaban kasar ya roki ‘yan majalisar su tantance wadannan nadin da ya yi.
Su wanene za su sa ido a EFCC?
Luqman Muhammad zai wakilci yankin Arewa maso gabas, yayin da Mista Anumba Adaeze zai wakilci Kudu maso gabas a majalisar hukumar ta EFCC.
Rahoton yace Alhaji Kole Raheem Adesina ne wanda zai wakilci Arewa ta tsakiya, sai kuma Alhaji Yahya Muhammad zai wakicli Arewa maso yamma.
Wannan ne karo na farko da za a rantsar da majalisar bayan shekaru shida da kafu war gwamnatin APC.
APC ta saki layi
Dazu nan aka ji cewa wani Jagoran APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa ya soki sauya-shekar Femi Fani-Kayode daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.
2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu
Vatsa yace jam’iyyar su ta APC tana jawo masu ‘Yan siyasar da aka ce barayin kasa ne a baya.
Asali: Legit.ng