Da dumi-dumi: Sarkin Kagara, garin da aka sace dalibai da malamansu ya rasu

Da dumi-dumi: Sarkin Kagara, garin da aka sace dalibai da malamansu ya rasu

- A yau ne labari ya fito cewa mai martaba Sarkin garin Kagara a jihar Neja ya rasu

- Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya wallafa rashin mai martaba sarkin Kagara a yau

- Shehu Sani ya bayyana jimaminsa da kuma yi wa sarkin addua'ar Allah ya bashi Aljanna

Mai martaba Sarkin Karaga na jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko ya rasu, The Nation ta ruwaito.

Tsohon Sanatan Kaduna, @ShehuSani ya tabbatar da rasuwar Sarkin a shafinsa na twitter a ranar Talata.

Ya ce, “Na samu labarin bakin ciki game da rasuwar Sarkin Kagara na Jihar Neja, Alhaji Salihu Tanko. Allah Ya ba shi gidan Aljanna firdausi. Amin. Inna lillahi wainna Illayhir rajiun.”

An nada Salihu Tanko a matsayin Sarki na 16 na Tegina a 1971.

KU KARANTA: Buhari, Osinbajo da sauran fitattun Najeriya za su yi rigakafin COVID-19 ranar Asabar

Yanzu-yanzu: Sarkin Kagara, garin da aka sace dalibai da malamansu ya rasu
Yanzu-yanzu: Sarkin Kagara, garin da aka sace dalibai da malamansu ya rasu Hoto: Duniyarmu A Yau
Asali: UGC

A ranar 1 ga Janairun 1982, an nada shi a matsayin Hakimin Kagara na biyu tare da matsayi mai daraja ta biyu domin ya gaji Alh Ahmadu Attahiru wanda ya rike mukamin har zuwa rasuwarsa a watan Nuwamba, 1981.

A ranar 1 ga Nuwamba 1991, Alh Salihu Tanko ya samu daukaka zuwa matsayin Sarki mai daraja ta daya a hannun Gwamnan jihar Neja Kanal Lawan Gwadabe.

KU KARANTA: Yajin aiki: Kayayyakin abinci sun yi tashin gwauron zabo a kudancin Najeriya

A wani labarin, Yan mata 317 da aka sace daga Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, sun dawo, in ji Gwamnan Jihar.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita cikin daren Talata, 2 ga Maris, 2021. A jawabinsa, ya bayyana irin jajircewan da suka yi domin ganin cewa an sako wadannan dalibai 317.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel