Manyan sarakunan arewa guda 6 da ‘yan bindiga suka sace

Manyan sarakunan arewa guda 6 da ‘yan bindiga suka sace

  • Kai farmaki ga shugabannin gargajiya tare da sace su ya zama gama gari a Najeriya musamman ma a yankin arewacin kasar
  • Zuwa yanzu miyagun sun yi garkuwa da sarakunan gargajiya da dama daga yankin arewa, amma dai sukan sako su daga baya
  • Na baya-bayan nan da suka sace shine Sarkin Bungudu na jihar Zamfara a kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna

Arewacin Najeriya - Matsalar sace-sacen mutane don karbar kudin fansa na kara kamari a Najeriya, inda ba a bar sarakuna ba ma musamman a yankin arewa.

Zuwa yanzu an sace sarakuna da dama daga yankin arewa wanda na baya-ayan nan da aka yi shine na Basaraken Bungudu a hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.

Manyan sarakunan arewa guda 6 da ‘yan bindiga suka sace
Manyan sarakunan arewa da ‘yan bindiga suka sace Hoto: Dailynigerian/Nigerian Tribune
Asali: UGC

Ga jerin wasu daga cikin sarakunan da mahara suka sace amma dai sun sako su illa na Bungudu da ke hannu a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

1. Sarkin Bungudu

A ranar Talata, 14 ga watan Satumba ne wasu Yan bindiga masu garkuwa da mutane a babban titin Abuja zuwa Kaduna sukayi awon gaba da Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da awon gaba da Sarkin tare da wasu dimbin mutane dake hanyar, rahoton Sun.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata a Kaduna.

Jalige ya kara da cewa yan bindigan sun budawa mutane wuta ne kan hanyar kafin awon gaba da su, amma har yanzu ba'a san adadin wadanda aka sace ba.

2. Sarkin Kajuru

A ranar 11 ga watan Yuli, 'Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Kajuru tare da 13 daga cikin iyalansa a wani samamen cikin dare da suka kai.

Kara karanta wannan

Yadda Yan bindiga suka yi awon gaba da Sarkin Bungudu a titin Kaduna/Abuja

An yi awon gaba da Alhaji Alhassan Adamu tsohon basarake mai shekaru 85 mai daraja ta biyu tare da matansa uku, jikokinsa biyu, hadimansa uku da wasu mutane biyar.

Yan kwanaki bayan haka kuma aka sako shi.

3. Sarkin Jaba

Bayan sarkin Kajuru, yan bindiga sun sake yin awon gaba da basaraken garin Jaba, Kpop Ham na masarautar Jaba, jihar Kaduna, mai suna Jonathan Danladi Gyet Maude.

Yan bindigar sun sace Maude ne a wani yankin jihar Nasarawa yayin wata ziyara da yakai jihar.

An kuma sako shi bayan kwana daya.

4. Dodo na Wawa

Har ila yau, 'Yan bindiga sun sace Mahmud Aliyu, Dodo na Wawa, sarkin gargajiya a garin New Bussa, hedkwatar karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Rahotanni sun ce an sace basaraken ne daga fadarsa a ranar Asabar.

Wasiu Abiodun, mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Neja, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar TheCable ranar Lahadi 5 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Daliban Zamfara 75 da aka sace sun samu 'yanci bayan kwanaki 11

5. Sarkin Rubochi

A watan Nuwamban 2019 yan sun yi awon gaba da wani babban basaraken gargajiya a babban birnin tarayya Abuja, Sarkin Rubochi, Mohammad Ibrahim Pada.

Sun sako shi bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan 6.5.

6. Sarkin Bukkuyum

Haka kuma a ranar 21 ga watan Maris din 2015 yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Bukkuyum mai Martaba Alhaji Muhammad Usman a jihar Zamfara.

'Yan bindigar sun sace sarkin a masallacin kofar gidansa bayan Sallar Magriba a ranar wata Juma'a, inda suka sako shi bayan ya shafe kasa da mako daya a hannunsu.

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

A wani labarin, mun kawo cewa masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan aure biyu a kauyen Piri da ke karamar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin garin mai suna Emos Bako, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:22 na daren ranar Lahadi, lokacin da masu garkuwa da mutanen suka mamaye unguwar.

Kara karanta wannan

Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi

Ya ce sun shiga gidan da karfi suka sace wata mata kafin su ci gaba da sace wata mata a unguwar da ke makwabtaka, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng