Masu garkuwa sun sallami Sarkin Rubochi bayan karbar kudin fansa N6.5m

Masu garkuwa sun sallami Sarkin Rubochi bayan karbar kudin fansa N6.5m

Gungun yan bindiga da suka yi awon gaba da wani babban basaraken gargajiya a babban birnin tarayya Abuja, Sarkin Rubochi, Mohammad Ibrahim Pada, sun sako shi bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan 6.5

Jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Larabar da ta gabata ne yan bindigan suka yi awon gaba da Sarkin bayan wani samame da suka kaddamar a garin Rubochi, inda suka kutsa kai har cikin gidan Sarkin suka sace shi.

KU KARANTA: Gwamna Matawalle ya fitar da daliban Zamfara 200 domin karo karatu a kasashen duniya

Wani dan uwan basaraken daya nemi a sakaya sunansa ya shaida ma majiyarmu cewa da misalin karfe 12 na ranar Asabar yan bindigan suka sako shi bayan kwashe tsawon kwanaki hudu a hannunsu, ya kara da cewa a dajin kauyen Gbawodi dake cikin karamar hukumar Toto na jahar Nassarawa suka ajiye.

“Da fari sun nemi kudin fansa naira miliyan 30, daga bisani suka sauko zuwa miliyan 25, amma da aka tsananta ciniki an tsaya a kan naira miliyan 6.5, daga nan aka dauki kudin aka mika musu.” Inji shi.

An hangi manyan yan fadan Sarkin Rubochi, masu rike da sarautun gargajiya, yan uwa da abokan arziki suna ta kwamba zuwa fadar Sarkin domin jajanta masa tare da nuna alhininsu bisa jarrabin data sameshi.

Wani babba a garin Rubochi ya koka kan matsalar rashin tsaro a yankin, inda yace: “Tsorona shi ne yan bindigan nan zasu fara tunanin wanda zasu dauke, musamman tunda dai sun amshi kudi masu tsoka kafin su saki Sarkinmu.”

A wani labarin kuma, wani jarumi daya shahara wajen kama barayi da miyagu a jahar Kaduna, Shehu Musa Aljan ya sake samun nasara yayin da yayi arangama da wasu gungun yan bindiga da suka tattara shanun mutane da nufin haurawa dasu gadar Kaduna.

Barayin sun sato dabbobin ne daga kauyen Rijana dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka yi kokarin tserewa dasu ta kan gadar rafin Kaduna, amma suka ci karo da Aljan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel