Yadda Yan bindiga suka yi awon gaba da Sarkin Bungudu a titin Kaduna/Abuja

Yadda Yan bindiga suka yi awon gaba da Sarkin Bungudu a titin Kaduna/Abuja

  • Bayan kwana biyu babu labarin sata, yan bindiga sun koma bababn titin Kaduna/Abuja
  • Tun bayan da aka aika jami'an Sojoji mata 300 hanyar aka samu sukuni
  • Yanzu kuma an yi awon gaba da Sarkin gargajiya a hanyarsa ta tafiya

Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun koma sace mutane a babban titin Abuja zuwa Kaduna yayinda sukayi awon gaba da Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru.

Masarautar Bungudu na jihar Zamfara, Arewa maso yammacin Najeriya.

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Bungudu a titin Kaduna/Abuja
Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Bungudu a titin Kaduna/Abuja
Asali: Facebook

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Hukumar yan sanda a jihar Kaduna ta tabbatar da awon gaba da Sarkin tare da wasu dimbin mutane dake hanyar, rahoton Sun.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata a Kaduna.

Yace:

"Yau,14 ga Satumba, misalin karfe 3:10 na rana hukumar yan sanda a Kaduna ta samu labarin garkuwa da mutane a kauyen Dutse, hanyar Kaduna-Abuja.
"An yi awon gaba da dimbin mutane yayinda mutum biyu suka jigata kuma suna jinya yanzu."
"Hakazalika labari ya nuna cewa sarkin Bungudu, a Zamfara, Alhaji Hassan Atto, na cikin wadanda aka sace."

Jalige ya kara da cewa yan bindigan sun budawa mutane wuta ne kan hanyar kafin awon gaba da su, amma har yanzu ba'a san adadin wadanda aka sace ba.

Hakazalika jami'in dan sanda daya ya rigamu gidan gaskiya

Yace an tura jami'ai wajen domin ceto wadanda aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng