Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sake Sace Wani Basarake a Jihar Kaduna
- Yan bindiga sun sake sace wani Basarake a jihar Kaduna mako biyu bayan sace sarkin Kajuru
- Ɓarayin sun yi awon gaba da basaraken ne yayin da ya fita duba gonarsa dake iyaka da jihar Nasarawa
- Kakakin yan sanda, ASP Muhammed Kiyawa, ya ce an ɗauke basaraken ne a wani wuri dake cikin nasarawa
An sake yin awon gaba da basaraken garin Jaba, Kpop Ham na masarautar Jaba, jihar Kaduna, mai suna Jonathan Danladi Gyet Maude, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Yan bindiga sun sace Maude ne a wani yankin jihar Nasarawa yayin wata ziyara da yakai jihar.
A rahoton channels tv, ɗan uwan basaraken, Anthony Maude ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar salula.
Yace: "An yi awon gaba da shi ne a gonarsa dake wani yanki da ake kira Gitata, jihar Nasarawa."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai har yanzun ba'a tabbatar da cewa basaraken shi kaɗai ya tafi gonar ko kuwa tare da masu tsaron shi ne.
Hukumar yan sanda ta tabbatar
Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, shine ya tabbatar da sace basaraken ga manema labarai.
Yace an sace Maude ne a yankin Panda, jihar Nasarawa yayin da ya kai ziyara domin duba gonarsa.
Wannan na zuwa ne mako biyu bayan wasu yan bindiga sun sace sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu.
Sai dai awanni 24 bayan sace shi ɓarayin suka sako shi amma sauran mutum 13 da aka kama sace su tare har yanzun suna hannun su.
Ɓarayin sun nemi a biya kuɗin fansa naira miliyan N200m kafin su sako mutanen dake hannunsu.
A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Saku Wasu Daga Cikin Daliban Sakandiren Bethel Baptist da Duka Sace a Kaduna
Yan bindiga sun sako ɗalibai 28 daga cikin waɗanda suke sace a makarantar sakandiren Bethel Baptist Damishi, Jihar Kaduna, bayan shafe kwanaki 20.
Shugaban ƙungiyar kiristoci CAN reshen Kaduna, Joseph Hayab, shine ya tabbatar da sako ɗalibai yau Lahadi.
Adadin ɗalibai 121 ne yan bindiga suka yi awon gaba da su a ɗakin kwanansu ranar biyar ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng