Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

  • 'Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace matan aure biyu a kauyen Piri da ke karamar hukumar Kwali, Abuja
  • Masu garkuwa da mutanen sun kai mamaya yankin ne da misalin karfe 11:22 na daren ranar Lahadi
  • Zuwa yanzu dai basu tuntubi 'yan uwan wadanda lamarin ya ritsa da su ba

Birnin tarayya, Abuja - Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan aure biyu a kauyen Piri da ke karamar hukumar Kwali ta birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin garin mai suna Emos Bako, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:22 na daren ranar Lahadi, lokacin da masu garkuwa da mutanen suka mamaye unguwar.

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2
Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2 Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya ce sun shiga gidan da karfi suka sace wata mata kafin su ci gaba da sace wata mata a unguwar da ke makwabtaka, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa

Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace, wanda ya so a sakaya sunansa, ya ce mijin daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su baya gida lokacin da lamarin ya faru, ya kara da cewa har yanzu ba a fara tattaunawa da masu garkuwa da mutanen ba.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya, ASP Daniel Y Ndiparya, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rundunar za ta tabbatar da ganin cewa an ceto mutanen.

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da magidanci da iyalinsa 4 a Kaduna sun nemi a biya naira miliyan 20

A wani labarin kuma, mun ji cewa masu garkuwa da mutanen da suka sace mutane biyar ‘yan gida daya a unguwar Sauri da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun bukaci a biya naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

An rahoto cewa maharan sun kai farmaki yankin ne inda suka yi awon gaba da wani mutum mai suna Peter Andrew Umoh, matarsa da kuma ‘ya’yansa guda uku.

Jaridar Daily Post ta kuma ruwaito cewa tsufa ya tilastawa ‘yan bindigar kyale mahaifin mutumin mai shekaru 86 a duniya. Sai dai kuma tsohon ya bayyana cewa a kaf danginsa gaba daya babu wanda yake da Naira miliyan 20 da maharan suka bukaci a biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng