Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13

  • Miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru dake jihar Kaduna
  • 'Yan bindigan sun sace sarkin, matansa 3, jikokinsa 2, hadimai 3 da wasu mutum 5
  • Sarkin ya kira taron jami'an tsaro inda ya sanar da shirin sacesa da ake yi amma ba a dauka mataki ba

Kajuru, Kaduna

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Kajuru tare da 13 daga cikin iyalansa a wani samamen cikin dare da suka kai, Sahelian Times ta ruwaito.

Alhaji Alhassan Adamu tsohon basarake ne mai shekaru 85 mai daraja ta biyu an yi awon gaba dashi tare da matansa uku, jikokinsa biyu, hadimansa uku da wasu mutum biyar.

KU KARANTA: Hotunan gwamnan Ogun yana gyara cunkoson titi da dare sun janyo cece-kuc

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13
Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13
Asali: Original

Daya daga cikin manyan masarautar wanda ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da aukuwar harin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daya daga cikin jikokin basaraken mai suna Saidu Musa mai rike da sarautar Dan Kajuru ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna

Ya ce 'yan bindigan sun kutsa gidan basaraken wurin karfe 12:30 na tsakar dare.

Sarki ya kira taron majalisar tsaro

An gano cewa ana gobe aukuwar lamarin, Sarkin ya kira taron gaggawa na tsaro kan kokarin da ake na sace shi, amma sai dai jami'an tsaro basu dauka mataki kan hakan ba.

Masarautar Kajuru tana da nisan tafiyar minti talatin daga garin Kaduna.

KU KARANTA: Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira

A wani labari na daban, Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, an zargesa da kange wasu bincike na zargin rashawa da ake wa wani gwamna mai ci yanzu da wasu tsoffin gwamnoni uku.

Kwamitin Jastis Ayo Salami ya ce yayin da Magu ke shugabantar EFCC, Magu "ya umarci jami'ai da kada su bincike" kan zargiin rashawa kan wasu mutum hudu, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allah Ya kunyata Abduljabbar tun a duniya - Mallam Muhammad Rijiyar Lemo

Tsoffin gwamnonin an gano sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano, Donald Duke na jihar Cross River da Ibikunle Amosun na jihar Ogun wanda yanzu haka sanata ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel