Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

  • Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama mawuyacin abu, a cewar Shugaba Muhammadu Buhari
  • Shugaban kasar ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar Imo
  • Buhari ya kuma ci gaba da cewa ba za a iya nuna masa yatsa na cin hanci da rashawa ba saboda ya kare kansa daga abubuwan yaudara

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, ya ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama mai matukar wahala.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a wani taro tare da shugabannin kudu maso gabas a Owerri yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar Imo.

Kara karanta wannan

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

Dalilin da ya sa yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ke da matukar wahala, Shugaba Buhari ya magantu
Shugaba Buhari ya ce yaki da cin hanci da rashawa na da matukar wahala Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya nakalto shugaban kasar a cikin wata sanarwa a shafin Facebook yana mai cewa babu wanda zai tuhume shi da mallakar kamfanoni ko manyan gidaje a ko ina cikin kasar nan.

A cewar Buhari, ya yi kokarin kare kansa ba tare da bata lokaci ba, ta yadda ba za a yin garkuwa da shi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari wanda ya rage masa kasa da shekaru biyu ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu ya ce idan ‘yan kasa suka samu tsaro, za su damu da harkokin gabansu ne.

Yayin da yake bayyana cewa zai yi duk abin da zai iya don ganin 'yan Najeriya masu aiki tukuru sun yi nasara a cikin ayyukan su, shugaban kasar ya ce zai ci gaba da kokarin barin gado na gaskiya da rikon amana a cikin tsarin.

Kara karanta wannan

Buhari: Igbo ne ke riƙe da tattalin arzikin Nigeria, sun fi iya kasuwanci

Buhari, ya kuma lura cewa yana son a tuna da shi a matsayin shugaban da ya daidaita Najeriya a fannin tsaro, ci gaban tattalin arziki, da samun nasara kan cin hanci da rashawa.

Ya ce:

Shugaban Najeriya Muhammadu yayin ziyarar aiki ta yini guda da ya kai jihar Imo a ranar Alhamis ya ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama mai matukar wahala.“Babu wanda zai zarge ni da mallakar kamfanoni ko manyan gidaje a ko’ina cikin kasar nan kuma ina godiya ga Allah da na yi kokarin tsaftace kaina yadda ya kamata, don kada a yi garkuwa da ni.
"Zan yi iya bakin kokarina don ganin 'yan Najeriya da ke kokari, sun yi nasara a kokarin da suke yi."

Buhari: Igbo ne ke riƙe da tattalin arzikin Nigeria, sun fi iya kasuwanci

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kabilar Ibo su na da fasaha tare da iya kirkire-kirkire, saboda hakan ne kuwa suke bada gudumawa mai tarin yawa wurin habaka tattalin arzikin kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Shugaban kasan ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wani taro da ya yi da shugabannin kudu maso gabas yayin ziyarar kwana daya da ya kai jihar Imo.

Kamar yadda takardar da Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar, shugaban kasan ya bukaci shugabannin kudu maso gabas da su wayar da kan mutanen su kan bukatar aiwatar da zabe na adalci da gaskiya a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel